Bauchi: Gobara ta barke a kasuwar Muda Lawal, wani ya mutu
Yanzu nan mu ka samu labari daga Channels TV cewa wuta ta kama kasuwar Muda Lawal da ke cikin garin Bauchi. A dalilin wannan gobara, an yi asarar rai da kuma dukiya.
Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, wannan wuta ta ci wani sashe na kasuwar ta Bauchi. Wannan mummunan abu ya auku ne a yau Alhamis, 16 ga watan Afrilu, 2020.
Wani Bawan Allah da gobarar ta barke a gabansa ya bayyana cewa wata katuwar mota da aka cika makil da katifu ne ta jawo gobarar bayan motar ta ci karo da igiyar wuta.
Wannan wuta ta shafe kimanin sa’a biyu ta na ci.
Shaguna da-dama na ‘yan kasuwa da abubuwan hawa sun kone. Haka zalika har an rasa ran mutum guda a gobarar.
Rahotanni sun bayyana cewa wani mutumi ya mutu inda wuta ta babbake shi ta yadda babu wanda zai gane kamaninsa. Muda Lawal ta na cikin tsofaffin kasuwannin jihar.
KU KARANTA: Wuta ta jawo asarar dukiya da takardun makaranta a Bauchi
Wasu Matasan da ke kasuwar sun aukawa ma’aikatan kwana-kwanan da su ka zo kashe wannan wuta.
Matasan sun ji haushin yadda masu kashe gobarar su ka iso a makare.
Daga baya masu kashe wutan sun koma sun karo kayan aiki da ma’aikata, kuma a karshe aka yi nasarar kashe gobarar. Kafin zuwansu dai an rasa dukiyoyi a ciki da gefen kasuwar.
Kawo yanzu ba a iya lissafa barnar da wannan wuta ta yi ba tukuna. Kasuwar Muda Lawal ta na cikin kasuwannin da ake ji da su a jihar Bauchi, kuma kasuwa ce da ta dade ta na ci.
Idan ba ku manta ba, ba a dade da samun labari cewa gobara ta ci kasuwar Ekotedo da ke garin Ibadan ba. A wannan kasuwa ma dai an yi asarar kaya da dukiyoyi na miliyoyin kudi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng