Coronavirus: Hon. Bago zai yi wa Mutanen Chachaga ruwan abincin azumi

Coronavirus: Hon. Bago zai yi wa Mutanen Chachaga ruwan abincin azumi

Ganin yadda azumi ya gabato a lokacin da ake fama da annobar Coronavirus, ‘Dan majalisar tarayya, Hon. Mohammed Umar Bago zai rabawa mutanensa tulin kayan abinci.

Honarabul Mohammed Umar Bago mai wakiltar Mazabar Chachaga a majalisar wakilan tarayya zai ba ‘Yan Mazabarsa kyautar manyan motoci har 11 cike da buhunan shinkafa.

Mohammed Bago ya bayyana cewa zai yi wannan ne domin fitar da mutane daga radadin wahalar da su ke ciki ganin an hana kowa fita a jihar Neja, sannan ga azumi ya gabato.

Bago ya ce babban Hadiminsa, Alhaji Abdulakeem Abdulrahman Oshinuga zai raba kayan. ‘Dan majalisar ya bayyana wannan ne a shafinsa na sada zumunta na Facebook jiya.

Kowace gunduma za ta samu mota guda cike da buhun shinkafa inji ‘Dan majalisar. Abdulakeem Abdulrahman Oshinuga zai dauki alhakin raba abincin ga duk Mabukatan yankin.

KU KARANTA: Ba don mu na so mu ka sadaukar da albashinmu ba - 'Dan Majalisa

Bago ya nuna damuwarsa ga rahoton da ya samu na cewa wani Bawan Allah a jiharsa ya kamu da cutar COVID-19. Wannan ne karon farko da aka samu Mai wannan cutar a Jihar.

A jawabin da ‘dan majalisar ya yi a Facebook, ya yi kira ga Jama’ansa su bi dokar kullen da Mai girma gwamna Abubakar Sani Bello ya sa domin hana yaduwar cutar Coronavirus.

Hon. Bago ya tabbatarwa mutanen da ya ke wakiltar a majalisar tarayyar cewa su na cikin ransa. ‘Dan siyasar ya ce ya na tare da jama’ansa a wannan mawuyacin hali da ake ciki.

Wannan gudumuwa ta zo ne jim kadan bayan da aka ji labarin cewa wani Kansila a jihar Neja ya tsere da buhunan kayan abincin da aka tanada domin marasa karfi a Garin Katcha.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng