Cutar Coronavirus ta kashe Faston da ya yi taurin-kai ya bude coci a Amurka

Cutar Coronavirus ta kashe Faston da ya yi taurin-kai ya bude coci a Amurka

Fitaccen Limamin cocin nan na kasar Amurka, Bishof Gerald Glenn wanda ya taba fitowa ya na cewa Ubangiji ya fi karfin cutar wata kwayar Coronavirus ya mutu a sanadiyyar cutar.

Jaridar New York Times ta rahoto mutuwar wannan Malamin addinin Kirista wanda ya na cikin wadanda su ka bijirewa matakan da aka sa domin rage yaduwar wannan muguwar cuta.

Mar-Gerie Crawley ta fitar da wani bidiyo inda ta tabbatar da mutuwar Mahaifinta wanda ya kasance ya na jagorantar cocin New Deliverance Evangelistic da ke Virginia a Amurka.

‘Diyar Marigayin ta ce Mahaifin na ta ya rasu ne a Ranar jajibirin bikin ‘Easter’ bayan ya kamu da cutar COVID-19. A sakamakon haka ya yi ta jinya a asibiti har dai ya ce ga garinku nan.

A Ranar 22 ga Watan Maris Bishof Glen ya yi wa Mabiyansa hudubar cewa ka da su ji tsoron wannan cuta. Jim kadan bayan wannan huduba, cutar ta kama Malamin ta kashe shi.

KU KARANTA: An hana Malaman asibiti zuwa gida bayan mutuwar Mai dauke da COVID-19

Gwamna Ralph Northam ya haramta haduwar mutane sama da 10 a lokaci guda amma wasu su ka yi watsi da wannan umarni, wanda hakan ya taimakawa yaduwar COVID-19.

Sama da mutum 180 su ka halarci hudubar da Faston ya yi a karshen Maris. Bayan nan ya kwanta rashin lafiya, ya rika numfashi da kyar. A karshe dai ya mutu bayan cutar ta ci karfinsa.

Wani Sanatan Amurka, Tim Kaine ya fito a shafinsa na Tuwita ya na ta jimamin rashin wannan Bawan Allah. Bishof Glen ya na cikin Bakaken fatan da su ka fara limanci a Yankin kasar.

Yanzu haka Mai dakin Marigayin watau Marcietia Glenn ta na dauke da cutar COVID-19. Kamar yadda wani Dattijo ya bayyana, ita ma ta bi sawun Mijinta inda ta ke kwance ta na jinya.

Ko da Marigayi Glenn ya bude coci kwanakin baya, ya haramtawa Jama’a gaisawa da juna. Glenn ya kuma yi kokarin nunawa Mabiyansa cewa su zama masu dogaro ga Ubangiji.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel