Lawan ya yiwa kakakin majalisa ta’aziyyar rashin surukarsa

Lawan ya yiwa kakakin majalisa ta’aziyyar rashin surukarsa

- Sanata Ahmad Lawan ya mika ta’aziyyarsa ga kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a kan mutuwar surukarsa

- Lawan ya kuma mika ta’aziyyarsa ga uwargidar Gbajabiamila da yan uwa da abokan arziki a kan rashin da suka yi

- Ya ce marigayiyar ta yi rayuwa mai inganci wajen yiwa al’ummanta hidima

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya mika ta’aziyyarsa ga kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a kan mutuwar surukarsa, Mildred Bisalla.

Lawan ya mika ta'aziyyar nasa ne a wani jawabi ta hannun hadiminsa na musamman a kafofin watsa labarai, Ola Awoniyi, a ranar Litinin 13 ga watan Afrilu.

Ya kuma mika ta’aziyya ga matar Gbajabiamila, iyalai da kuma abokan arziki a kan rashin da suka yi.

Lawan ya yiwa kakakin majalisa ta’aziyyar rashin surukarsa
Lawan ya yiwa kakakin majalisa ta’aziyyar rashin surukarsa
Asali: UGC

Har ila yau ya kuma yi ta’aziyya ga gwamnati da mutanen jahar Plateau da darikar Anglican inda Bisalla ta kasance mamba.

Lawan ya bayyana cewa Bisalla wacce ta kasance ma’aikaciyar jinya kuma ma’assashiyar kungiyar Plateau Nigerian Horticultural Society, ta yi rayuwa mai inganci a matsayinta na ginshiki ga iyalai da al’ummanta.

Yayinda take yiwa marigayiyar addu’a, Lawan ya roki Allah ya ba wadanda ta bari juriyan rashin ta.

KU KARANTA KUMA: FG ta fadi ranar da 'yan N-Power za su fara samun alat

A wani labari na daban, mun ji cewa an kashe tsohon shugaban karamar hukumar Ganye na rikon kwarya, Sabastine Kaikai a sa'o'in farko na ranar Talata.

'Yan bindigan dai sun je har gidan tsohon shugaban karamar hukumar da ke kauyen Kaikai na karamar hukumar Ganye, inda suka aika dashi lahira.

Kamar yadda jaridar The Nation Online ta bayyana, har yanzu dai ba a san dalilin kisan nashi ba.

An gano cewa Sabastine Kaikai ya ziyarci kauyen ne don hutun bikin Easter amma sai ya iske ajalinsa bayan sa'o'i kadan da isarsa.

Kamar yadda makwabtansa suka bayyana, "Yan bindigar sun isa ne da tsakar dare inda suka fara harbin iska kafin su gaggauta shiga gidansa".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng