Shugaban kasar Ukraine ya sa kyautar kudi ga wanda ya binciko maganin Coronavirus

Shugaban kasar Ukraine ya sa kyautar kudi ga wanda ya binciko maganin Coronavirus

A yayin da annobar COVID-19 ta jefa al’umma cikin wani hali. Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya yi alkawarin makudan kudi ga wanda ya ceci Duniya.

Volodymyr Zelensky ya sha alwashin bada gagarumar kyauta ta Dala miliyan 1 ga duk wani Mai bincike da nazari da ya iya hada kwayar maganin da zai yaki cutar COVID-19.

Kakakin shugaban kasar ta bayyana wannan a Ranar Litinin, AFP ta fitar da wannan rahoto. Ukraine wanda a da ta ke cikin Daular Rasha ta na cikin wanda annobar ta taba.

A halin yanzu sama da mutum 3, 000 su ka kamu da wannan cuta a Ukraine mai mutane miliyan 42. Daga cikin wadanda cutar ta kama, an samu mutane kusan 100 da ta kashe.

Shugaba Zelensky ya na ganin cewa fam miliyan guda ta Dalar Amurka ta isa tukwuici ga wanda ya gano maganin wannan cuta, inji Mai magana da yawunsa, Yuliya Mendel.

A wani jawabi da Yuliya Mendel ta aikawa AFP, ta ce Mai gidanta ya na kokarin ganin an kirkiro maganin da zai ceci rayukar dinbin al’umma daga wannan muguwar cutar.

KU KARANTA: Kasashen da su ka fi gamuwa da tashin hankalin annobar COVID-19 a Afrika

Shugaban kasar Ukraine ya sa kyautar kudi a binciko maganin Coronavirus
Gwamnatin Ukraine ta sa tukwuicin kudi domin gano maganin COVID-19
Asali: Instagram

Misis Yuliya Mendel ta ce shugaba Zelensky ya na so ya hada-kai da Masana domin su fito da maganin cutar. Shugaban ya aikawa Masanan kasar wannan roko a Watan jiya.

Zelensky ya aika takarda ga Cibiyar Masana kimiyya na kasar Ukraine inda ya ke bukatarsu da su zage dantse wajen binciko maganin da zai rika kashe kwayar cutar COVID-19.

Mendel ba ta bayyana yadda za a samo wannan kudin tukwuici ba. A halin yanzu tattalin arzikin Ukraine ya na tangal-tangal saboda yaki da kasar ke yi da masu tada kafar baya.

“A halin yanzu ba za mu yi magana dalla-dalla game da inda za a samo wannan kudi ba.” Inji Mai magana da yawun shugaban kasar da ya dare kan mulki a tsakiyar shekarar 2019.

Idan ba ku manta ba tuni gwamnatin Ukraine ta bada umarnin rufe duk wasu kananan makarantu da jami’o’i, an kuma hana jirgin kasa yawo domin rage yaduwar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel