Covid-19: Ba za mu iya rufe arewa ba - Gwamnoni

Covid-19: Ba za mu iya rufe arewa ba - Gwamnoni

A ranar Litinin ne gwamnonin jihohin arewa suka gudanar da wani taro domin tattauna tasirin annobar cutar covid-19 a yankin.

An gudanar da taron ne ta hanyar amfani da fasahar kiran waya na bidiyo mai hada mutane da yawa.

Bayan kammala tattaunawa da musayar ra'ayi a kan kalubalen da kowacce jiha ke fuskanta, shugaban kungiyar gwamnonin, Simon Lalong, ya fitar da jawabi a kan matakan da gwamnonin suka dauka.

Darektan yada labaran gwamna Lalong, Dakta Macham Makut, ya fitar da jawabin ranar Litinin, inda yace gwamnonin sun yanke shawarar kara matakan tsaro a kan iyakokinsu.

Hakazalika tare da hada karfi wajen karfafa matakan dakile yaduwar annobar.

"Yanzu dai gwamnonin arewa sun amince a kan cewa kowacce jiha za ta dauki matakan da suka dace da jama'arta, saboda rufe yankin zai zo da babban kalubale, musamman idan aka yi la'akari da cewa mafi yawan 'yan arewa manoma ne da ke bukatar zuwa gona a yayin da aka fara ruwan sama.

Covid-19: Ba za mu iya rufe arewa ba - Gwamnoni

Gwamnonin arewa
Source: Twitter

"Kazalika, gwamnonin sun tattauna a kan tallafin jin kai da gwamnatin tarayya ke bayarwa, inda suka bayyana rashin jin dadinsu a kan rashin bawa jihohin yankin tallafi duk da an samu bullar annobar covid-19 a wasu jihohin yankin.

DUBA WANNAN: Hana fita da taron jama'a: An kama babban Limami, an kwace motoci 269 a Abuja

"Gwamnonin sun nuna fargaba damuwarsu a kan yadda suka yi amfani da kudaden aljihunsu wajen tallafawa jama'a, tare da bayyana cewa ba za su iya cigaba da hakan ba matukar gwamnatin tarayya ba ta sakar musu kudi kamar yadda ta sakarwa wasu jihohin ba."

"Gwamnonin sun sake nuna damuwarsu a kan rashin cibiyar gwajin cutar covid-19 a yankin arewa."

Sun lashi takobin hada kai da gwamnatin tarayya domin ganin kowacce jiha ta samu cibiyar gwaji a kalla guda daya. "

Bayan tattaunawa a kan tasirin annobar covid-19 a kan tattalin arzikin Arewa, gwamnonin sun yanke shawarar kafa kwamitin mutane 7 a karkashin gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu,

Kwamitin za ta nemowa yankin mafita daga cikin lamarin.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da gwamnonin jihohin Kaduna, Sokoto, Nasarawa, Jigawa, Gombe da Nasarawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel