COVID-19: Wasu ‘Yan Najeriya da ke shirin barin kasar Ingila sun kamu da Coronavirus
Akalla mutanen Najeriya 10 cikin 40 da aka yi wa gwajin COVID-19 na tilas ne a kasar Birtaniya aka gano cewa su na dauke da kwayar cutar Coronavirus, Punch ta ruwaito
A ranar Litinin ne aka fitar da sakamakon gwajin da aka yi a Landan, wanda ya nuna wadannan mutane da yanzu ba su nuna wata alamar rashin lafiya sun kamu da cutar.
Wannan ya tada hankalin Jami’ai domin kuwa akwai yiwuwar cewa wadannan bayin Allah sun yada cutar ga wasu mutane ba tare da su kansu sun san sun kamu ba.
A cewar rahoton, labarin gwajin ya rikita Jami’an ofishin Jakadancin Najeriya da wasu da ke babban birnin Landan a Birtaniya.
A halin yanzu akwai mutanen Najeriya fiye da 2, 000 da ke watse a kasashe irinsu Amurka, Ingila, Sin, da UAE da su ke rokon gwamnati ta dauko su ta dawo da su kasarsu.
Ma’aikatar harkokin kasar waje ta ce dole sai dai wadannan Mutane su biya kudin jirginsu da kansu, sannan kuma sai an yi masu gwajin COVID-19 kafin su shigo Najeriya.
KU KARANTA: An sake samun mutane 20 da ke dauke da COVID - 19 a Najeriya
A haka ne dai aka samu mutane goma da suke da niyyar dawowa Najeriya dauke da wannan cuta a Ingila. Hakan na nufin dole a killace wadannan jama'a da kuma na-kusa da su.
Da-dama daga cikin wadanda su ka fita kasashen waje su ka makale a wannan lokaci ‘Daliban Makaranta ne da kuma manyan ‘Yan kasuwan da ke fita ketare yin fatauci.
Majiyar ta ce tuni an killace wadannan mutane har sai sun samu sauki.“Mun samu labarin sakamakon gwajin sahun farko na mutane 40 da su ka yi rajistar a dawo da su Najeriya. Sakamakon ya nuna mutane 10 su na dauke da cutar COVID-19.”
“Abin da ke jawo dar-dar shi ne watakila sun yada wannan mummunar cuta ga wasu mutanen.” Inji ta.
Kakakin hukumar da ke kula da ‘Yan Najeriya da ke kasashen ketare, Abdul-Rahman Balogun, ya tabbatarwa ‘Yan jarida wannan, ya ce ana kula da masu dauke da cutar a Ingila.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng