Shugaba Boris Johnson ya godewa Ma’aikatan asibiti bayan an sallame shi

Shugaba Boris Johnson ya godewa Ma’aikatan asibiti bayan an sallame shi

- Firayim Ministan kasar Birtaniy, Boris Johnson ya samu sauki, har kuma an sallame shi daga asibiti.

- Boris Johnson ya yi fama ne da jinyar cutar COVID-19 kwanan nan a asibiti.

Boris Johnson ya fitar da jawabin farko a Ranar Asabar ya na godewa Ma’aikatan kiwon lafiyan gwamnati da ke asibitin St. Thomas inda aka kwantar da shi tun makon da ya wuce.

Bayan ya fito, shugaban na Birtaniya ya godewa Likitoci da sauran Malaman asibitin da su ka cecei rayuwarsa. Ya ce: “Ba zan iya gode masu yadda ya dace ba. Sun ceci rayuwata.”

Wannan na karon farko da Firayim Ministan ya yi wa mutanen kasarsa jawabi tun bayan da aka kwantar da shi a gadon asibiti. An kwantar da Johnson ne a Ranar Lahadin da ta wuce.

Johnson ya shaidawa Jama’a cewa ya kamu da cutar COVID-19 a Ranar 27 ga watan Maris.

KU KARANTA: COVID-19 ta shiga jikin wani Mai Gadi a Jihar Kaduna

Shugaba Boris Johnson ya godewa Ma’aikatan asibiti bayan an sallame shi
Asibitin St. Thomas da Boris Johnson ya yi jinya a Landan
Asali: Twitter

Shugaban kasar Turan ya cigaba da aiki daga gidansa da ke tsakiyar Birnin Landan duk da cewa ya kamu da COVID-19. Sai dai a wannan lokaci bai iya shiga cikin bainar Jama’a.

Daga baya ne jikin Johnson ya tabarbare, aka ruga da shi asibiti a birnin na Landan.

A Ranar Litinin Likitoci su ka maida shi sashen da ake kai wadanda jikinsu yayi tsanani.

A Ranar Alhamis ne aka fito da Firayim Ministan daga sashin ICU kamar yadda Kakakin gwamnatin Birtaniya ya shaida. Kakakin gwamnatin ya ce shugaban na su ya wartsake.

Zuwa Ranar Juma’a, Boris Johnson ya fara tafiya ya na zagayawa. Bayan jikinsa ya kara karfi ne aka sallame shi daga asibitin, ya kuma yi ban-kwana da Likitocin da su ka duba sa.

CNN ta bayyana cewa a zuwa Ranar Asabar, akwai mutane 9, 875 da cutar Coronavirus ta kashe a Ingila. Kusan mutane 80, 000 ne wannan mummunar cuta ta kama a halin yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel