Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kubutar da mutane 18 a Zamfara

Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kubutar da mutane 18 a Zamfara

Dakarun rundunar soji na atisayen 'Hadaran Daji' sun kubutar da mutane 18 da masu garkuwa da mutane suka sace a jihar Zamfara.

Rundunar sojojin ta kubutar da mutanen, da suka hada da maza 10, mata 4 da kananan yara 4, yayin harin da suka kai wa 'yan bindigar a tsakanin Maru zuwa Dansadau.

Kazalika, an kashe yan bindigar 9 yayin atisayen da aka yi wa lakabi 'Chingaba'.

A wani atisayen da rundunar soji ta gudanar a kauyen Sarwa da ke karamar hukumar Isah a jihar Sokoto, sojoji sun kashe gagararren mai safarar bindigu da ake kira da 'Alhaji'.

A wani jawabi da jagoran atisayen sojoji, Manjo Janar John Enenche, ya fitar, ya bayyana cewa, "dakarun rundunar sojin kasa da hadin gwuiwar na sojin sama sun kaddamar da wani hari a kan 'yan bindiga a Zamfara, a karkashin wani atisaye mai taken 'chingaba'.

Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kubutar da mutane 18 a Zamfara
Dakarun Sojoji
Asali: UGC

"Yayin harin, wanda aka kai a yankin Maru zuwa Dansadau, sojoji sun kashe 'yan bindiga 9 tare da kubutar da mutane 18 da aka yi garkuwa da su."

Jawabin ya kara da cewa, "a wani harin da dakarun soji suk kaddamar ranar 11 ga watan Afrilu, 2020, a kauyen Sarwa da ke karkashin karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto, an kama wani gagararren mai safarar bindiga da ake kira Alhaji.

DUBA WANNAN: 'Na ji jiki', Kauran Bauchi ya bayyana halin da ya shiga a cibiyar killacewa bayan ya kamu da covid-19

"Sai dai, yaransa sun budewa dakarun soji wuta a harin kwanton bauna da suka kai domin kubutar da shi.

"An harbe shi, ya mutu, yayin da yaransa suka gudu da raunukan harbin bindiga. Dakarun soji sun samu bindiga kirar GPMG PKT, harsashi dari da arba'in, kwanson alburushi guda hamsin da babur guda daya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel