Sake duba lissafin kasafin kudin 2020 zai jawo dogon Turanci a Majalisar Tarayya
‘Yan majalisar tarayya sun nuna mabanbantan ra’ayoyi game da kwaskwarimar da gwamnatin Najeriya ta ke bukatar a yi wa kasafin kudin kasar na wannan shekara.
Shugaban kasa Muhammmadu Buhari ya rattaba hannu a kan kasafin kudin bana tun a Disamban 2019, amma yanzu an dawo da kundin kasafin gaban majalisa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya tana so ayi wa kasafinta wasu gyare-gyare ne bayan barkewar annobar Coronavirus. da kuma illar da tayi tattalin arzikin kasa.
A ranar Larabar da ta gabata ne Ministar tattalin arziki, Zainab Ahmed Shamsuna, ta mikawa majalisa kasafin kudin kasar da tsarin tattalin arzikin MTEF da FSP.
Wasu ‘Yan majalisar kasar sun shaidawa Jaridar Daily Trust cewa ya zama dole a sake duba kasafin kudin ganin irin halin da tattalin arzikin Najeriya ya shiga yanzu.
Sanata Abdullahi Kabir Barkiya mai wakiltar Katsina ta tsakiya ya nuna cewa babu abin mamaki don gwamnati ta rage kasafin kudin da ta yi a sakamakon karyewar mai.
KU KARANTA: Jama’a su cigaba da zama a gidajensu har sai nan gaba - Buhari
Abdullahi Kabir Barkiya ya ce kashi 85% na tattalin arzikin Najeriya ya dogara ne da arzikin man fetur. A yanzu kuma, farashin mai ya karye a kasuwar duniya.
Wani Sanatan APC mai wakiltar Taraba, Yusuf A. Yusuf ya bayyana cewa za su duba kwaskwarimar da gwamnatin tarayya ta ke so ayi idan har sun dawo zama.
Sanata Yusuf A. Yusuf ya nuna cewa ‘Yan majalisa za su rage wasu abubuwa da gwamnati ta saka a kasafin, kuma za su kara wasu abubuwa da aka manta da su a kundin.
‘Dan majalisar na jihar Taraba ya bayyana cewa za su duba ayyuka masu muhimmanci wanda za su babbako da tattalin arzikin kasar tare da samar da ayyukan yi ga mutane.
Honarabul Solomon Maren mai wakiltar Yankin Mangu da Bassa a majalisar wakilai ya nuna rashin jin dadi game da wasu ayyukan da aka cire daga kasafin kudin na bana.
Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta rage burin da ta ci na kashe Naira tiriliyan 10.5 a abana saboda halin da aka shiga. Abin da wasu ‘Yan majalisa ba za su so ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng