Shugaba Buhari ya roki ‘Yan Najeriya su ki cigaba da zama a gida a lokacin annoba
A jiya Asabar ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga mutanen kasar nan da su ka cigaba da zama a cikin gidajensu yayin da ake ta fama da annobar COVID-19.
Shugaban kasar ya fitar da jawabi ta bakin Mai magana yawunsa watau Garba Shehu, inda ya shaidawa mutanen Najeriya cewa gwamnatin tarayya za ta cigaba da kawo dauki.
Malam Garba Shehu ya tabbatar da cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari za ta kai wa mutanen Legas, Ogun da babban birnin tarayya agaji sakamakon halin da su ke ciki.
Makonni biyu da su ka wuce kenan da gwamnatin tarayya ta hana shiga da fita a wadannan wurare. Shugaban kasar ya dauki wannan mataki ne domin hana yaduwar COVID-19.
Da ya ke magana a jiya Ranar 11 ga Watan Afrilu, shugaban kasar ya godewa ‘Yan Najeriya a game da hakurin da su ka yi, da kuma jajircewa wajen ganin karshen wannan annoba.
KU KARANTA: Buhari ya ja kunnen Sojoji game da cin zarafin Jama'a a lokacin kulle
“Mun fahimci cewa a yau akwai ‘Ya ‘yan da ba za su iya kai wa Iyayensu da Manyansu ziyara ba saboda killacesu da aka yi. Kuma akwai wadanda su ke rayuwar hannu-baka-hannu-kwarya da su ka shiga cikin wani halin kunci a wannan yanayi.”
“Babu gwamnatin da aka zaba ta za ta bukaci wani abu daga Mabiyanya fiye da abin da mu ka roka daga wajenku. Amma dole mu sake rokonku – Ku takaita yawace-yawace a wuraren da aka bada umarni. Haka kuma dole mu bi dokokin da Masana da Ma’aikatan asibti su ka gindaya – A zauna a gida, a rika wanke hannuwa, a ceci rayukan jama’a.”
Shugaban kasar ya nuna cewa za a dakatar da wannan takunkumi da zarar Masana kimiyya sun bada shawarar yin haka, amma dai a yanzu an dauki wannan mataki a fadin Duniya.
“A yanzu hakkinmu ne mu fada maku gaskiya karara, akwai annoba da ta shiga kasashe 210. Ba za mu tsaya mu na jiran wasu su kawo mana dauki wajen yakar kwayar cutar nan ba.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng