A kaina kawai dokokin Afakallah ke aiki - Adam Zango

A kaina kawai dokokin Afakallah ke aiki - Adam Zango

Shahararren dan wasan Hausa kuma mawakin zamani Adam A. Zango, ya fede biri har wutsiya game da dangantakar da ke tsakaninsa da hukumar tace fina-finai ta jahar Kano.

Zango ya bayyana cewa saboda shine hukumar ta kirkiro wasu dokokinta.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, jarumin ya kuma bayyana dalilinsa na yin rajista da hukumar, wadda ke karkashin jagorancin Alh. Isma'il Na'abba Afakallah.

Ya ce ya yi rajistar ne ba domin komai ba sai saboda yaransa su dunga samun aikin shirya fina-finai.

A cewarsa, an daina gayyatar yaran nasa zuwa aikin shirya fim tun bayan lokacin da ya bayyana ficewar sa daga masana’antar shiya fina-finai ta Kannywood.

A kaina kawai dokokin Afakallah ke aiki - Adam Zango
A kaina kawai dokokin Afakallah ke aiki - Adam Zango
Asali: Facebook

Zango ya yi bayani kamar haka: "Na dawo na yi rajista da hukumar tace Finafinai ne a dalilai guda biyu. Na farko shi ne furodusana da su ke fim da ni a Kano sun fi yawa, sannan kuma yarana da ke zaune da su, wadanda na ke mu'amala da su, abokai na duk su na samun matsala, ba a kiran su ayyuka a dalilin wadannan abubuwa da ban yi ba.

"Wasu ma sun yi rajista, amma saboda su na tare da ni ba sa samun ayyuka.

"To sai na ga menene dalilin da ba zan yi ba? Idan na yi, ba don wani kudin shiga zan ce na yi ba. Amma me zai hana na yi don wadannan mutanen sun dade su na bibiya ta.

"Magana ta gaskiya, ban taza zama na yi tunanin hakan ba; sai a 'yan kwanakin nan da su ka wuce ne naga cewar to wadannan mutanen gaskiya kamar na shiga hakkin su ne, saboda su na yin fina-finai da ni.

"A ciki akwai wanda ba ya yin fim da wani jarumi sai ni, amma a dalilin ban yi rajista ba ya hakura ya daina."

Ya ci gaba da cewa: "Sai su ka rinka yin ayyukan da wasu jarumai, amma kuma jaruman su na ba su matsala, su na cika musu kudi, su na yi musu wulakanci, wanda hakan ya sa ban ji dadi ba.

"In da kamar a ce na yi rajista, kenan ba za a samu wannan matsala ba. Daga baya na yi tunani na ce bari in je na yi rajistar."

Zango ya yi gargadin cewa kada fa a dauka ya dawo cikin masana'antar finafinan Hausa ne.

Mujallar fim ta ruwaio inda ya ke cewa: "Kuma hakan ba shi ne ya nuna na dawo Kannywood ba.

"Har yanzu ina nan a matsayi na na mai cin gashin kan sa, saboda hukumar ba ta ce dole sai ka na ƙarƙashin Kannywood za ka je ka yi rajista ba.

"Ina so mutane su san cewar dangantaka ta da abokan sana'a ta ya na nan, ba ni da wata matsala da kowa, kungiya ce ta Kannywood da ba za ta iya kwato mini 'yanci na ba na ce na daina, ba na yi!"

Dangane da dokokin hukumar tace Finafinai ta jahar Kano kuwa, a nan ne jarumin ya yi kakkausar suka, ya yi nuni da cewa ana bambanta shi da sauran 'yan fim.

Zango ya ce: "Ka'idojin da hukumar ta gindaya ya na kan dukkan jarumai da mawaƙa da su ka yi rajista. Nawa ba zai bambanta da na kowa ba, duk da dai wasu lokutan dokokin da ya ke kai na bai kan kowanne jarumi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An sake samun wani da ya mutu sakamakon coronavirus a Lagas

"Kamar yadda aka yi a kwanaki na haska fim ɗin Rahama Sadau, ka ga ai wannan Rahama kan ta ma ba ta da rajista, amma ta kira masoyan ta su zo su kalli fim, ta yi tallan fim din ta kuma an zo an kalla.

"Amma ni zuwa zan yi, ba ni da alaƙa da fim din, jarumi ne kawai ni, zan zo na ba ta gudunmawa ne na kira jama'a su zo su kalla, amma aka dakatar da ni.

"To ka ga doka ne ba a kan kowanne jarumi ba, nawa daban ne.

"Ita Rahama fim din ta ne fa, kudin sule biyar ba zai shiga aljihu na ba a matsayina na Adam A. Zango."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel