COVID-19: Likitan da ya mutu a Katsina ya yi mu’amala da sarakunan gargajiya da wasu manyan mutane

COVID-19: Likitan da ya mutu a Katsina ya yi mu’amala da sarakunan gargajiya da wasu manyan mutane

Rahotanni sun kawo cewa likita mai zaman kansa da ya rasu a yankin Daura, jahar Katsina sakamakon cutar coronavirus, Dr Aliyu Yakubu, ya yi mu’amala da sarakuna da manyan mutane kafin mutuwarsa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, lokacin da marigayin ya dawo Katsina daga jahar Lagas kafin a kwantar dashi a asibitin sojin sama, ya yi mu’amala da mutane da dama.

Da fitowar labarin mutuwar Dr. Yakubu sakamakon cutar coronavirus, tsoro da fargaba ya shiga zukatan mutane kan yiwuwar yaduwar cutar a jahar.

A kan haka, shugaban kungiyar matasan Najeriya reshen jahar Katsina, Lukman Kankia, da shugaban Cliqq Media Enterprise, Jamilu Mabai, sun yi kira ga rufe dukkanin harkoki a garin Daura domin hana yaduwar cutar.

An kuma tattaro cewa wani abun damuwa kan lamarin mutuwar likitan, shine wadanda suka aiwatar da shirin gawarsa har zuwa ga binne shi.

Sannan cewa likitoci da malaman jinya da suka kula da shi a lokacin da yake jinya, suma ya zama dole a gano wadanda suka yi mu’amala da su domin hana yaduwar cutar.

A kan haka, Gwamna Aminu Bello Masari na jahar, yayinda ya ke karin haske kan lamarin, ya ce a yanzu an killace mutane 35 sannan ana kula da su sakamakon mu’amala da suka yi da marigayin.

COVID-19: Likitan da ya mutu a Katsina ya yi mu’amala da sarakunan gargajiya da manyan mutane
COVID-19: Likitan da ya mutu a Katsina ya yi mu’amala da sarakunan gargajiya da manyan mutane
Asali: Facebook

Ya ce wadanda aka killace sun hada da wasu daga cikin marasa lafiyan da marigayin ke kula da su, iyalansa da wasu mutane da suka je ta’aziyyarsa bayan ya mutu.

Ya kara da cewar an dauki samfurin jininsu sannan cewa jahar na jiran sakamakon gwajin nasu.

Masari ya ce samun sakamakon gwajin nasu ne zai sa gwamnati ta dauki matakin gaggawa, imma na killce dukkanin jahar ko kuma wasu yankunan jahar domin hana yaduwar cutar.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: NCDC ta karyata batun kashe N1bn don aikewa yan Najeriya da sakonnin waya

A wani labarin kuma, mun ji cewa an sake sallamar wasu majinyata 7 da suka warke daga cutar coronavirus daga cibiyar killacewa ta jihar Legas.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ne yayi sanarwar a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis kuma jaridar The Nation ta wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng