Shugaban kasar Najeriya ya yi wa Enahoro, Alli, Effiong da wasu Sojoji afuwa

Shugaban kasar Najeriya ya yi wa Enahoro, Alli, Effiong da wasu Sojoji afuwa

Shekaru da dama bayan mutuwarsu, gwamnatin tarayyar Najeriya ta yafewa Farfesa Ambrose Alli da Cif Anthony Enahoro a rana daya da aka yi wa wasu da ke gidan yari afuwa.

Ministan harkokin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya sanar da wannan mataki da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauka a yau Ranar 9 ga Watan Afrilu, 2020.

Ga jerin wadanda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa afuwar bayan sun bar Duniya:

1. Anthony Enahoro

Cif Anthony Enahoro ya na cikin wadanda su ka taimaka wajen karbowa Najeriya ‘yanci. Enahoro ‘Dan siyasa ne tun jamhuriya ta farko. A 1962 aka kama shi da wasu ‘Yan siyasar AG da laifin kitsa kifar da gwamnatin Abubakar Tafawa-Balewa, wannan ta sa Enahoro ya tsere daga Najeriya.

Anthony Enahoro ya rike Ministan sadarwa da kwadago da kuma Ministan harkokin na musamman a gwamnatin Sojan Yakubu Gowon. Da su aka kafa jam’iyyar NPN, ya rasu a 2010.

KU KARANTA: COVID-19: An bada damar zuwa wuraren ibada a Jihar Kogi

2. Ambrose Alli

Farfesa Ambrose Folorunsho Alli Farfesan Likita ne wanda ya zama gwamna tsakanin 1979 zuwa 1983 a jihar Bendel. Bayan Janar Muhammadu Buhari ya yi juyin-mulki, ya kama gwamnan da laifin satar kudin kwangila, wannan ya sa ya yanke masu daurin shekaru 100 a kurkuku.

Shugaban kasar Najeriya ya yi wa Enahoro, Alli, Effiong da wasu Sojoji afuwa
Buhari ya yafewa na hannun-daman Awolowo bayan shekaru 58
Asali: Twitter

3. Lt. Col. Moses Effiong

Laftanan Kanal Moses Effiong ya na cikin manyan Sojojin da aka samu da laifin yunkurin yi wa gwamnatin Ibrahim Babangida juyin mulki a 1986. Moses Effiong wanda ainihinsa mutumin Kuros Riba ne ya na cikin wadanda ake yankewa hukuncin kisa tare da Janar Mamman Vatsa.

A gidan kurkukun Kano aka ajiye Moses Effiong har ya yi ta fama da rashin lafiya. Sauran wadanda aka yankewa hukunci tare da shi sun hada da Chris Oche, Mike Iyorshe, Martin Luther, Asen Ahura; Daniel Bamidele, Akwashiki, V.E. West, Jonathan India Garba da wasu Sojoji uku.

Sauran wadanda gwamnatin Najeriya ta yi afuwa a wannan rana su ne: Major E.J. Olanrewaju da kuma Ajayi Olusola Babalola, dukkansu sun gito ne daga Yankin Kudu maso Yammacin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel