Wani dan majalisa ya bayar da naira miliyan 1.5 domin a gina Masallaci a Katsina

Wani dan majalisa ya bayar da naira miliyan 1.5 domin a gina Masallaci a Katsina

- Dan majalisa mai wakiltan mazabar Maiadua a majalisar dokokin jahar Katsina, Malam Mustapha Rabe, ya bayar da tallafin naira miliyan 1.5 don a gina Masallaci

- Rabe ya ce za a gina Masallacin ne a kauyen Muludu a kokarinsa na cika alkawaran zaben da ya dauka

- Ya kuma raba wa talaka 100 kudi N5,000 a mazabarsa domin su habbaka kasuwancinsu

Rahotanni sun kawo cewa wani dan majalisar dokokin jahar Katsina, Malam Mustapha Rabe, ya bayar da tallafin naira miliyan 1.5 domin gina Masallaci a kauyen Muludu da ke mazabarsa.

Da yake gabatar da kudin a ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu, Rabe wanda ya kasance dan APC mai wakiltan yankin Maiadua, ya ce hakan na daga cikin kudirinsa na cika alkawaran zaben da ya dauka.

Wani dan majalisa ya bayar da naira miliyan 1.5 domin a gina Masallaci a Katsina
Wani dan majalisa ya bayar da naira miliyan 1.5 domin a gina Masallaci a Katsina
Asali: Depositphotos

“Burina shine hada kan garuruwa da mutane masu akida daban-daban ta fannin addini da asali, ta yadda za a hadu wajen gina zaman lafiya da hadin kai.

“Kamar yadda annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “duk wanda ya gina wani dakin Allah, Allah zai gina masa mafificin haka a aljannah,” in ji shi.

Ya bukaci al’umman mazabarsa da su ci gaba da zaman lafiya da kuma tsafta sosai ta hanyar wanke hannayensu da sabulu da ruwa, da kuma nisantan taron jama’a da amfani da takardar fayce majina da kaurinsu idan suna tari ko atishawa.

Dan majalisar ya kum raba N5,000 ga talakawa 100 domin habbaka kasuwancinsu a mazabarsa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Najeriya ta karbi sawu na 2 na kayan agajin annobar Coronavirus daga China

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta janye dokar dakatad da Sallar Juma'a a jihar bayan ganawar shugabannin addini, sarakunan gargajiya da jami'an tsaro a jhar.

Hakan ya biyo bayan mutuwar wani Likita mazaunin garin Daura, Dakta Aliyu Yakubu, sakamakon cutar a makon nan.

Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa, a jawabin da ya saki ranar Laraba ya ce an janye dokar dakatad da Sallolin Juma'a amma akwai sharruda da aka kindaya na kiwon lafiya da tsaro.

A cewarsa, an shawarci Limaman Juma'a su takaita hudubobinsu domin sallamar Masallatai cikin kankanin lokaci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel