Dr. Ngozi Iweala ta jinjinawa yadda ake raba kayan abinci a kasar Ruwanda

Dr. Ngozi Iweala ta jinjinawa yadda ake raba kayan abinci a kasar Ruwanda

Tsohuwar Ministar tattalin arzikin Najeriya, Dr. Okonjo-Iweala ta shiga cikin wadanda su ke magana game da halin da Duniya ta samu kanta a daidai wannan lokaci.

Najeriya da sauran kasashen Duniya su na fama da cutar COVID-19. A dalilin haka ne Attajiran Bayin Allah da gwamnati su ke taimakawa Marasa karfi da kayan abinci.

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta yi tsokaci a game da yadda mutanen kasar Ruwanda su ke tallafawa mutanen da ba su da karfi domin rage masu radadin da su ka samu kansu.

Okonjo-Iweala ta yi kira a kaikaice ga 'Yan Najeriya da sauran Jama’a su yi koyi da wannan salo na kasar Ruwanda inda ake raba abinci ba tare da an samu wani cunkoso ba.

Dr. Okonjo-Iweala wanda ta rike kujerar Ministar kudi har sau biyu a Najeriya a gwamnatin Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan ta wallafa wannan a shafinta dazu.

KU KARANTA: Za a zakulo wadanda su ka dawo daga kasar waje a Sokoto

Tsohuwar Darektar babban bankin Duniyar ta yaba da wannan kokari da ake yi a kasar Afrikan wajen raba abinci ga masu kananan karfi ba tare da an jawo cincirindo ba.

A cewar ta, wannan abin koyi ne ganin yadda abinci da sauran kayan bukatu su ke kai ga Bayin Allah har gidajensu ba tare da sun fito waje ba a yayin da ake zaman kulle.

Kamar yadda shafin na ta na dandalin zumuntan Facebook ya nuna, Okonjo-Iweala ta wallafa wannan hoto ne da kusan karfe 1:00 na yau Laraba, 8 ga Watan Afrilu, 2020.

A halin yanzu dai babu wanda cutar COVID-19 ta kashe a kasar Ruwanda. Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan annoba ta hallaka mutane biyar daga karshen bara zuwa yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel