Bankin Duniya zai ba ba Najeriya $82m domin inganta harkar lafiya - REDISSE

Bankin Duniya zai ba ba Najeriya $82m domin inganta harkar lafiya - REDISSE

Najeriya za ta samu wasu kudi masu yawa daga babban bankin Duniya domin bunkasa sha’anin lafiya. An soma ba Najeriya wannan kudi da nufin habaka harkar kiwon lafiyar kasar.

A wani jawabi da bankin ya fitar a Ranar Talata, 7 ga Watan Afrilu, 2020, an ba Najeriya fam Dala miliyan 82 ta wani shiri na REDISSE da aka kawo domin inganta harkar kiwon lafiya.

Hukumomi sun nemi alfarmar bankin ya kawowa Najeriya agajita yadda za a gyara asibitoci cikin watanni shida. Bankin ya bayyana wannan a babban birnin tarayya da ke Abuja.

Ana kyautata zaton za a yi amfani da wadannan kudi da sun haura Naira Biliyan 29 wajen gyara asibitocin gwamnati a yanzu da Najeriya ta ke ta fama da annobar cutar Coronavirus.

“Bada gudunmuwa ga hanyoyin samun abincin jama’a da kuma taimakawa kananan ayyukan na samun abin kashewa a cikin shekaru biyun nan zai taimaka wajen rage radadin tattali.”

KU KARANTA: Za a lalubo mutanen da Likitan da Coronavirus ta kashe ya yi alaka da su

Bankin Duniya zai ba ba Najeriya $82m domin inganta harkar lafiya - REDISSE

Za a tallafawa tattalin arzikin Najeriya da shirin REDISSE
Source: Facebook

Bankin ya nuna cewa Najeriya za ta bukaci wannan agaji na tsawon makonni 18 zuwa 24. Har zuwa lokacin, za a cigaba da fama da tasirin da annobar cutar COVID-19 ta yi a kasar.

“Tare da Abokan hulda, bankin na tattaunawa da jihohi da gwamnatocin jihohi da hukumomin tarayya domin ganin yadda za a taimakawa Marasa karfi wajen harkar samun kudin."

Jawabin ya kuma nuna cewa za a yi amfani da wannan Dala miliyan 82 domin taimakawa gidajen da ba su da hali. Za kuma a agazawa masu kanana da matsakaicin kasuwanci.

“Ta shirin REDISSE, har an narka wasu Dala miliyan 10.6 domin taimakawa hukumar NCDC mai kokarin takaita yaduwar cututtuka a Najeriya wajen gyara wasu dakunan aikinsu.”

Jawabin ya kara da cewa bayan gyara dakunan ko-ta-kwanan hukumar, ana sayen kayan aikin da za ayi amfani da su a dakunan killace jama’a da ke fadin Jihohi akalla 12 a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel