COVID-19: Gwamnatin Ribas ta kama wadanda su ka tuka jirage bayan haramta tashi

COVID-19: Gwamnatin Ribas ta kama wadanda su ka tuka jirage bayan haramta tashi

Gwamnan jahar Ribas, Nyesom Wike, ya yi umurnin kama wasu matukan jirgin sama mai saukar ungulu su biyu kan zargin take dokar da gwamnatin jahar ta bayar, domin hana yaduwar annobar coronavirus a jahar.

Kotun majistare na Port Harcourt ta kuma tsare su a gidan yari, yayinda gwamnan ya kaddamar da cewar zai ajiye rigar kariyar da yake da shi a gefe domin shaida a kan duk wanda ya saba dokar rufe iyakar jahar.

Ya bayyana hakan ne a ofishin kwamishinan yan sandan Ribas, Mustapha Dandaura, a Port Harcourt, a ranar Talata, 7 ga watan Afrilu, biyo bayan kama matukan jirgin wanda Wike ya ce sun shiga jahar ba bisa ka’ida ba.

A cewar kungiyar ma’aikatan jirgi na Najeriya, matukan jirgin na muhimmin aiki ne na mai da gas, kamar yadda hukumar jirgin sama na Najeriya (NCAA) ta yarje masu.

COVID-19: Gwamnatin Ribas ta kama wadanda su ka tuka jirage bayan haramta tashi
COVID-19: Gwamnatin Ribas ta kama wadanda su ka tuka jirage bayan haramta tashi
Asali: UGC

Da take martani kan lamarin, kamfanin jirgin mai saukar ungulu, ta ce daga ita har abokan kasuwancin nata sun samu yardar yin tafiya da ci gaba da harkokinsu ta bangaren masana’antar mai da gas.

A wani jawabin manema labarai, kamfanin ta ce an sanar da ita cewar Gwamna Wike zai zo ya yi jawabi ga ma’aikatan a Port Harcourt don haka sai suka tsaya.

“Amma da ya iso, sai gwamnan ya yi umurnin kama matukanmu su biyu a kai su sashin CID, inda aka bukaci su rubuta jawabai sannan cewa za a tsare su har zuwa 19 ga watan Mayu,” in ji kamfanin.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Hukumar kwastam ta saki tireloli 247 dankare da kayan abinci da ya kai naira biliyan 3.2

Don haka sun roki gwamnatin tarayya da ta sa gwamnatin jahar Ribas ta saki matukansu wanda a cewarsu, basu taka kowani doka ba.

A wani labarin kuma, mun ji cewa hukumar kula da hadurra ta tarayya ta ce an kama masu laifi 321 sakamakon take dokar hana walwala da suka yi a wasu jihohin kasar nan.

Jami’in wayar da kai na FRSC, Bisi Kazeem, ya bayyana hakan ne a wata takarda da ta fita a ranar Talata. Ya ce an yi kamen ne daga ranar 30 ga watan Maris zuwa 6 ga watan Afirilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng