COVID-19 ta kashe wani Likitan Katsina da ya dawo daga Legas –Masari
A yayin da cutar COVID-19 ta ke cigaba da jefa jama’a a cikin halin ha’ula’i, ba a bar Najeriya a baya ba. An samu mutane sama da 200 da su ka kamu a kasar Yammacin Afrikan.
Rahotanni sun zo mana cewa wannan cuta ta kashe wani Likita a asibitin Sojoji da ke Daura, jihar Katsina. Wannan ne karon farko da za a rasa rai a sanadiyyar annobar a Yankin.
Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana labarin wannan mutuwa a farkon makon nan. Mai girma gwamna Aminu Bello Masari ya fitar da wannan jawabi da kan shi a Yau Talata.
Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya ce wannan Likita da ke aiki a wajen jihar ya rasu a Ranar Asabar. Gwajin da aka yi bayan ya rasu, ya nuna ya na dauke da kwayarcutar COVID-19.
KU KARANTA: Masu dauke da cutar COVID-19 a kasar Saudi za su haura 200, 000
A cewar Aminu Masari, Marigayin mai suna Aminu Yakubu ya na aiki ne a wani asibitin kansa da ya bude a Daura kafin rasuwarsa. Ainihin Marigayin Mutumin jihar Kogi ne.
Gwamnatin Katsina ta bayyana cewa Dr. Aminu Yakubu ya mutu ne bayan ya kai kan shi asibitin Sojojin sama a Daura. Sai dai bai kara sa'a biyu ba a a asibitin, sai ya ce ga garinku nan.
Garin Daura da ke jihar Katsina ne Mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari. Kafin yanzu ba a samu wani da ya rasu ko ma akalla ya kamu da cutar Coronavirus a Katsina ba.
Idan ba ku manta ba kwanaki gwamna Aminu Masari da mataimakinsa watau Mannir Yakubu su ka yi gwajin cutar COVID-19, kuma sakamako ya nuna ba su kamu da cutar ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng