Ministan lafiyan Saudi ya bayyana yadda annobar Coronavirus za ta barke

Ministan lafiyan Saudi ya bayyana yadda annobar Coronavirus za ta barke

A dalilin annobar cutar Coronavirus, an fara shakkun yin aikin hajji da aka saba kowace shekara a kasar Saudi Arabiya mai tsarki. Saudi ta na cikin kasashen da cutar ta addaba.

A Ranar Talata ne Ministan lafiya na kasar Saudi Arabiya ya yi gargadin cewa annobar Coronavirus za ta yi kamari. Ministan ya ce dubannan mutane za su kamu da cutar.

Mai girma Minista Tawfig AlRabiah ya yi wannan bayani ne jim kadan bayan gwamnatin Saudi ta kara wa’adin takunkumin da aka sa na zaman gida a wasu manyan Biranen kasar.

Saudi ta dauki matakin hana yawo ne domin takaita yaduwar wannan mummunar cuta mai jawo wahalar numfashi. Amma duk da haka Ministan ya ce mutane 200, 000 za su kamu.

Gidajen yada labaran kasar sun rahoto AlRabiah ya na cewa: “A cikin ‘yan makonnin nan, hasashen ya nuna cewa wadanda za su kamu da cutar za su kai 10, 000 zuwa 20, 000.”

KU KARANTA: Coronavirus ta dauki sabon salon shiga jikin mutane a Najeriya

Ministan lafiyan Saudi ya bayyana yadda annobar Coronavirus za ta barke
Ministan lafiya na kasar Saudi Arabia Tawfig AlRabiah
Asali: Twitter

Ministan lafiyar ya nayyana cewa kasar Saudi Arabiya ta na cikin wani mawuyacin hali wajen yaki da kwayar cutar COVID-19 a yanzu kamar yadda wannan bincike ya nuna masu.

Wannan bincike ya yi la’akari ne da wasu nazari da kwararrun kasar Saudiya da wasu wadanda ake ji da su a kaashen Duniya su ka yi. Masana hudu ne su ka yi wannan binciken.

Saudi ce ta fi kowace kasa cikin kasashen Larabawan Yankin fama da wannan cuta. Akalla mutane 2, 700 su ka kamu da cutar. Alkaluma sun nuna COVID-19 ta kashe mutane 41.

A jiya Ma’aikatar cikin gidan kasar Saudi Arabiya ta hana fita gaba daya a Garuruwan Riyadh, Tabuk, Dammam, Dhahran sa Hofuf. Haka zalika Jeddah, Taif, Qatif da kuma Khobar

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng