Annobar COVID-19: Buhari ya na neman Dala Biliyan 3.4 daga bankin Duniya, IMF

Annobar COVID-19: Buhari ya na neman Dala Biliyan 3.4 daga bankin Duniya, IMF

Domin ganin bayan annobar cutar Coronavirus gwamnatin Najeriya ta dauki matakai na musamman. Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta na neman aron Biliyan $3.4.

Jaridar Daily Trust ta ce shugaban kasa Buhari ya na neman wannan makudan kudi wanda sun haura Naira tiriliyan 2.53 domin ceto kasar daga wannan annobar cuta da aka shiga.

Ministar tatattali da kasafin kudin Najeriya, Zainab Ahmed Shamsuna ta bayyana wannan a Abuja lokacin da ta zanta da wasu ‘Yan jarida game da matakan da za a dauka a kasar.

Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta dauki matakin nemo wannan kudi ne saboda karyewar da farashin mai ya yi a kasuwar Duniya, tare da muguwar annobar da ta dabaibaye ko ina.

Domin rage radadin tattalin da Najeriya za ta samu kanta, Najeriya za ta yi kar-kaf da abin da ke cikin asusunta na hukumar IMF. Gwamnati ta na neman Dala biliyan 3.4 daga asusun.

KU KARANTA: Gwaji ya nuna wata Damisa ta kamu da cutar COVID a Amurka

Annobar COVID-19: Buhari ya na neman Dala Biliyan 3.4 daga bankin Duniya, IMF

Buhari zai nemi bashi domin yaki da annobar COVID-19 a Najeriya
Source: Twitter

Ministar kudin ta bayyana cewa ta mika takarda gaban IMF domin a ba kasar kudin da ta ajiye a asusun hukumar. Ministar ta ce ba za a sa wani shardai wajen karbar wannan kudi ba.

Bayan haka kuma gwamnatin tarayya za ta karbo aron kudi Dala biliyan 2.5 daga babban bankin Duniya. Sannan Najeriya za ta aro wasu Dala biliyan 1 daga wajen bankin cigaban Afrika.

Ahmed ta jaddada cewa wannan kudi za su taimakawa Najeriya wajen aiwatar da abubuwan da ta yi niyya a kasafin 2020. Jihohin kasar za su amfana da Dala biliyan 1.5 daga cikin kudin.

Sai dai Ministar kasar ba ta shaidawa Duniya adadin kudin da gwamnati za ta nema daga bankin Musulunci ba. Amma gwamnati za ta karbe gaba daya abin da ta mallaka a asusun IMF.

A daidai wannan lokaci da abin da ake samu daga danyen mai zai ragu da kusan Naira biliyan 400, gwamnati za ta ciro Dala miliyan 150 daga cikin lalitar NSIA domin a cike gibin FAAC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel