Masu garkuwa da mutane sun bukaci a biya miliyan 20 kafin su saki hadimin Gwamna Sule

Masu garkuwa da mutane sun bukaci a biya miliyan 20 kafin su saki hadimin Gwamna Sule

- Yan bindigan da suka sace hadimin gwamnan Nasarawa, John Mamman, sun bukaci da a biya kudin fansa naira miliyan 20 kafin su sake shi

- Da fari masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya naira miliyan 150 kafin su sake shi , amma daga bisani suka rage kudin

- An tattaro cewa a lokacin da masu garkuwan suka kira iyalansa, sun jiyo muryar Mamman, yana rokon afuwa

Yan bindigan da suka yi garkuwa da mai ba gwamnan jahar Nasarawa shawara ta musamman kan kananan hukumomi, Mista John Mamman, sun bukaci a biya kudin fansa naira miliyan 20 kafin su sake shi.

Sun kuma bukaci a saki daya daga cikin mambobinsu da jami’an tsaro suka kama ko kuma su kashe hadimin gwamnan, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ku tuna cewa a ranar Asabar da misalin karfe 8:00 na dare ne aka sace Mamman a gidansa da ke Dari a karamar hukumar Kokona da ke jahar.

Masu garkuwan wadanda suka kai mamaya gidan nasa, sun yi ta harbi ba kakkautawa domin su tsoratar da mutane kafin suka yi nasarar tafiya dashi.

Masu garkuwa da mutane sun bukaci a biya miliyan 20 kafin su saki hadimin Gwamna Sule
Masu garkuwa da mutane sun bukaci a biya miliyan 20 kafin su saki hadimin Gwamna Sule
Asali: Twitter

Sai dai kuma sun taki rashin sa’a yayinda wasu yan garin suka kama daya daga cikinsu sannan suka mika shi ga yan sanda.

Wata majiya ta kusa da ahlinsa sun ce masu garkuwa da mutanen sun bukaci naira miliyan 150 ne da farko, inda daga bisani suka rage zuwa naira miliyan 20 a yanmmacin ranar Litinin.

KU KARANTA KUMA: Boko haram sun kai hari wani gari a Adamawa, sun kona gidaje

An tattaro cewa a lokacin da masu garkuwan suka kira iyalansa, sun jiyo muryar Mamman, yana rokon afuwa.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Tsohon dan takarar kujerar gwamnan jihar Legas, Babatunde Gbadamosi, ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Legas sakamakon take dokar hana walwala da jihar ta gindaya.

An damke Gbadamosi ne bayan da aka ganshi a bidiyon liyafar zagayowar ranar haihuwar Abdul-Rasheed Bello, mijin 'yar wasan Nollywood, Funke Akindele. An yi liyafar ne a rukunin gidaje da ke Amen a Ibeju-Lekki da ke jihar Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel