Boko haram sun kai hari wani gari a Adamawa, sun kona gidaje

Boko haram sun kai hari wani gari a Adamawa, sun kona gidaje

- Mayakan Boko Haram sun kai farmaki wani kauye a karamar hukumar Madagali da ke jahar Adamawa

- Sun kai harin ne a garin Kirchinga da yammacin ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu

- Mazauna yankin sun ce yan ta'addan sun yi ta harbi a sama tare da sace kayayyaki a shaguna, sannan kuma kona gidaje

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa mayakan kungiyar ta'adda na Boko Haram, sun kai farmaki wani kauye a karamar hukumar Madagali da ke jahar Adamawa.

Mazauna garin Kirchinga inda a nan ne aka kaddamar da harin, sun bayyana a ranar Talata, 7 ga watan Afrilu cewa mayakan na Boko Haram sun kai farmaki kauyen a yammacin ranar Litinin, sannan suka fara kona gidaje da sata a shaguna.

Wani mazaunin yankin ya ce mayakan na Boko Haram sun isa kauyen da daddaren ranar a cikin manyan motoci da babura, jaridar The Nation ta ruwaito.

Boko haram sun kai hari wani gari a Adamawa, sun kona gidaje
Boko haram sun kai hari wani gari a Adamawa, sun kona gidaje
Asali: Depositphotos

“Sun zo suna ta harbi a sama sannan suka yi ta sata a shaguna da kona gidaje yayinda mutane suka tarwatse domin neman tsira,” in ji shi.

Wata majiya kuma ta ce ba don sojoji sun shiga lamarin ba da ba karamin ta’adi yan ta’addan za su yi ba.

“Sojoji sun bayyana bayan dan wani lokaci sannan hakan ya sa yan ta’addan saurin tserewa,” in ji majiyar.

KU KARANTA KUMA: Dokar hana fita: Wani dan sanda ya kashe ma’aikacin gidan mai

Da yake tabbatar da lamarin kwamandan rundunar sojin a Madagali, Kanal US Abdulsalam ya ce, “an kai wani hari amma an yi nasarar dakile shi."

A gefe guda mun ji cewa Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby ya yi kira ga shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, da ya fito daga maboyarshi tare da mika kanshi ko kuma a halaka shi a hakan. Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da Deby ya jagoranci rundunar sojin kasar Chadi don ragargaza mayakan.

Wannan samamen kuwa ya yi ajalin a kalla 'yan ta'adda 92 kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A wani jawabi da shugaban kasan yayi wa jama'ar kasar shi, ya yi magana da harshen Faransanci tare da cewa Shekau yana da damar miko kanshi ko kuma za a zakulo shi daga maboyar shi tare da kashe shi kamar yadda aka yi wa kwamandojinshi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rundunar sojin kasar Chadi ta kai wa 'yan ta'adda hari inda ta halaka mayaka 92.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel