Gwaji ya nuna Damisa ta kamu da COVID-19 a gidan dabbobin New York

Gwaji ya nuna Damisa ta kamu da COVID-19 a gidan dabbobin New York

Wata Damisa mai suna Nadia ta zama dabbar dajin farko da ta kamu da cutar COVID-19 a Duniya. Nadia ta na killace ne a wani gidan ajiye dabbobi da ke Garin New York a Amurka.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa Nadia mai shekaru hudu da haihuwa ta kamu da kwayar cutar COVID-19. Kafin yanzu dai ba a san wata dabbar dawa da ta kamu ba.

Ku na sane cewa COVID-19 cuta ce da ake kamuwa da ita daga kwayar Coronavirus. Mutane da dabbobin gida su kan yi fama da wahalar numfashi idan sun kamu da COVID-19.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, akwai wasu dabbobin jeji da su ka hada da ‘Yaruwar wannan Damisa da wasu Zakoki da ake zargin sun kamu da cutar Coronavirus.

Damisar mai shekara hudu ta rika fama da busasshen tari ne kwanaki. Wannan ya sa aka yi mata gwajin kwayar cutar COVID-19 wanda sakamako ya nuna cewa ta na da cutar.

KU KARANTA: Coronavirus: Guardiola ya rasa Mahaifiyarsa a Barcelona

Gwaji ya nuna Damisa ta kamu da COVID-19 a gidan dabbobin New York
An gano Coronovirus ta shiga jikin wata Damisa a Amurka
Asali: UGC

Wadannan dabbobin dawa da ke killace a gidan dabbobin Bronx Zoo a birnin New York su na fama da irin wannan tari kamar yadda hukumar da ke kula da dabbobin jeji ta fada.

Hukumar WCS ta bayyana cewa ana sa ran wadannan sauran dabbobi har su biyar – Damisa biyu da Zakoki uku za su warke daga tarin da su ke yi tare da fama da rashin karfin jiki.

Ko da ba a taba jin labarin COVID-19 a jikin Damisa ko Zaki ba, Likitoci su na kula da dabbobin a halin yanzu, kuma su kan yi wasa da masu ba su abinci kamar yadda su ka saba.

Wani babban Likitan dabbobin ya bayyana cewa wannan ne karon farko da COVID-19 ta kama irin wannan dabbobin. Ana zargin daga wurin wani ‘Dan Adam Nadia ta dauki cutar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng