Coronavirus: Har yanzu ba a tabbatar da sakamakon gwaji na biyu da aka yiwa Gwamna Mohammed ba – Mataimakin gwamna

Coronavirus: Har yanzu ba a tabbatar da sakamakon gwaji na biyu da aka yiwa Gwamna Mohammed ba – Mataimakin gwamna

Yayinda ake ci gaba da rade-radi kan sakamakon gwajin Gwamna Bala Mohammad na jahar Bauchi a karo na biyu, kwamitin gwamnatin jahar kan Coronavirus ya bayyana cewa har yanzu ba a tabbatar da sakamakon gwajin gwamnan na biyu ba.

Hakan na zuwa ne a lokacin da kwamitin ya sanar da kudirin jahar na samar da cibiyar gwajin cutar Coronavirus.

Gwamnatin ta yi ikirarin cewa ana samun tsaiko ne saboda wahala da jinkirin da ke tattare da kai samfurin jini hedkwatar cibiyar hukumar hana yaduwar cututtuka na Najeriya (NCDC) a Abuja domin gwaji da sakamako.

Mataimakin gwamna Sanata Baba Tella wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu a Bauchi yayinda ya ke yi wa manema labarai karin bayani kan COVID-19 ya tabbatar da cewar akwai mutane uku da suka kamu a jahar.

Coronavirus: Har yanzu ba a tabbatar da sakamakon gwaji na biyu da aka yiwa Gwamna Mohammed ba – Mataimakin gwamna
Coronavirus: Har yanzu ba a tabbatar da sakamakon gwaji na biyu da aka yiwa Gwamna Mohammed ba – Mataimakin gwamna
Asali: Twitter

Sai dai kuma ya ce hukumar NCDC bata riga ta sanar da sakamakon gwajin Gwamna Bala Mohammed na biyu ba.

Gwamna Bala dai ya shafe makonni biyu Cif a killace.

Sanata Bala yayinda yake bayani kan cewa NCDC bata bayyana ko gwamnan na dashi ko baida shi a yanzu, ya gargadi jama’a da su guji yarda da bayanai da suke samu a soshiyal midiya.

KU KARANTA KUMA: Kasar Ghana za ta kara wa ma’aikatan jinya kaso 50 na albashi da kuma yafe wa mutane kudin ruwa

A cewarsa gwamnan na cikin koshin lafiya kuma cewa ya shiga sahun tattaunawar kungiyar gwamnoni ta kafar Skype.

Tella ya bayyana cewa jahar ta yi gaggarumar nasara wajen gano mutane 305 da suka hadu biyo bayan barkewar cutar a jahar amma ana sanya ran samun sakamako mai kyau.

A gefe guda mun ji cewa yayinda jihar Kaduna ta samu karin mai cutar Coronavirus daya ranar Lahadi, wanda ya kai adadin masu cutar a jihar 5, gwamnatin jihar ta ce kawo yanzu an tura sanfurin jinin mutane 89 Abuja domin gwaji.

Kwamishanar kiwon lafiyan jihar, Dakta Amina Mohammed Baloni, wacce ta bayyana hakan ranar Litinin ta ce cikin samfura 89 da aka tura, sakamakon ya nuna 5 sun kamu, 77 basu kamu ba, kuma ana sauraron 8.

Baloni a jawabin da ta saki ranar Litinin ta ce kawo yanzu an katabta sunayen mutane 119 da ake nema.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel