Campbell: Duniya ta yarda cewa mun yi zaben gaskiya a 2011 – Jonathan

Campbell: Duniya ta yarda cewa mun yi zaben gaskiya a 2011 – Jonathan

Kwanakin baya tsohon Jakadan kasar Amurka a Najeriya, John Campbell ya yi wani rubutu inda ya yi zargin cewa magudi ya yi a zaben 2011, wanda Goodluck Jonathan ya lashe.

Daily Trust ta fitar da rahoton cewa tsohon shugaban Najeriyar ya yi maza ya maidawa John Campbell martani inda ya wanke kansa daga zargin magudin zaben da jefa sa da shi.

Dr. Goodluck Jonathan ya yi jawabi ne ta bakin Mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze. Mista Eze ya ce duk wadanda su ka sa-ido a zaben 2011, sun tabbatar cewa an gaskiya aka yi.

Eze ya ke cewa har hukumomin Amurka da wadanda su ka lura da zaben Najeriya daga kasashen ketare sun gamsu da cewa zaben 2011 ne ya fi kowane sahihanci a lokacin tun 1999.

Goodluck Jonathan wanda ya lashe wannan zabe da John Campbell ya nuna shakku game da ingancinsa, ya bayyana cewa gaskiyar zaben ta sa duk Alkalai su ka ba sa nasara a kotu.

KU KARANTA:

Campbell: Duniya ta yarda cewa mun yi zaben gaskiya a 2011 – Jonathan

John Campbell ya na da shakku a zaben 2011 da Jonathan ya yi nasara
Source: Depositphotos

Hadimin tsohon shugaban kasar ya ce Alkalai sun ga raguwar 75% na korafin zaben da su ka saba karba a kotu bayan zabukan Najeriya don haka ya ce an yi zabe mai nagarta a 2011.

“Babu shakka ‘Yan Najeriya da su ka haura shekaru 45 sun san labarin zabukan da aka yi a 1999, 2003, 2003, 2007, 2011, 2015 da 2019 – kuma sun fi cancanta su auna kyawun zabukan.”

Jawabin Eze ya ce mutanen Najeriya ne za su yi magana game da ingancin zabukan da aka yi ba Campbell ba. Hadimin tsohon shugaban ya nuna akwai son kai a maganar Jakadan.

Jawabin ya ce duk wanda ya damu da Najeriya bai kamata ya rika tado wannan maganar da aka riga aka bizne. Jonathan ya ce abin da ke gabansa shi ne kara inganta harkar zabe a yau.

Rahoton ya ce ba wannan ba ne karon farko da Hadiman Jonathan su ka samu matsala da John Campbell wanda ya zama Jakadan Amurka a Najeriya tsakanin shekarar 2004 da 2007.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel