Coronavirus: Yan sanda sun kama ango da amarya saboda karya doka

Coronavirus: Yan sanda sun kama ango da amarya saboda karya doka

Rahotanni sun kawo cewa jami’an ‘yan sanda a kasar Afirka ta Kudu sun kama wani ango da amaryarsa da malamin coci da kuma baki 40 da suka karya dokar hana fita da hukumomi suka sanya domin hana yaduwar cutar coronavirus.

Mutanen dai sun karya dokar inda suka halarci daurin auren a lardin KwaZulu Natal, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

A bisa ga wani bidiyo da kafar yada labarai ta Afirka ta Kudu eNCA ta wallafa, an gano amaryar a cikin motar ‘yan sanda sanye da tufafin daurin aurenta.

Coronavirus: Yan sanda sun kama ango da amarya saboda karya doka
Coronavirus: Yan sanda sun kama ango da amarya saboda karya doka
Asali: UGC

An kai dukkan mutanen ofishin ‘yan sanda da ke kusa da Richards Bay. Sannan a ranar Litinin za a tuhume su kan laifn karya doka.

KU KARANTA KUMA: Farashin diesel da kananzir ya ki sauka duk da karyewar farashin mai

Afirka ta Kudu, wacce ta tabbatar mutum 1,655 sun kamu da coronavirus, ta ce mutum 11 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar, ko da yake tana daga cikin kasashen duniya da suka fi tsaurara dokar hana fita.

A wani rahoton kuma mun ji cewa Kungiyar NMA ta Likitocin Najeriya da kuma TUC ta ‘Yan kasuwa sun nuna rashin amincewar su da gayyatar da gwamnatin tarayya ta yi wa Likitoci da Ungonzoma daga kasar Sin.

Wadannan kungiyoyi sun nuna cewa sam ba su tare da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a wannan mataki da ta dauka na yaki da cutar Coronavirus da ta addabi kasashe.

A Ranar Juma’ar da ta gabata ne Ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire, ya shaidawa Najeriya cewa wasu Malaman kiwon lafiya daga kasar Sin za so Najeriya domin taimakawa asibitocinmu.

Bayan haka, Osagie Ehanire, ya bayyana cewa za a aikowa Najeriya kayan aikin asibiti wanda daga cikin har da na’urar taimakawa numfashi, wannan duk don a yaki cutar COVID-19.

Sai dai shugaban kungiyar Likitoci a Najeriya, Dr. Francis Faduyile, a wani jawabi da ya fitar wanda ya shiga hannun Daily Trust, ya nemi gwamnati ta dakatar da wannan magana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng