Ana neman Gwamna Matawalle ya koma Jam’iyyar APC a Zamfara

Ana neman Gwamna Matawalle ya koma Jam’iyyar APC a Zamfara

Bayan karkare duk wata shari’a a kotu game da zaben gwamnan jihar Zamfara, mun samu rahoto cewa maganar janye gwamna Bello Matawalle zuwa jam’iyyar APC ta na kara karfi.

Daily Trust ta fitar da wani rahoto a Yau wanda ya bayyana cewa wasu ‘Yan siyasa a jihar Zamfara su na ta kiran Mai girma gwamna Bello Matawalle ya yi watsi da jam’iyyar PDP.

Matawalle ya zama gwamna a bagas ne a sakamakon rikicin cikin gidan da ya ci jam’iyyar APC a zaben 2019. A dalilin haka ne APC ta tashi war-was duk da ta samu mafi yawan kuri'u.

Tun bayan darewar Matawalle kujerar gwamna aka fara kiran ya sauya-sheka. Tsohon gwamna kuma jigon APC Ahmad Sani Yarima, ya na cikin wadanda su ka fara yin wannan magana.

Kwanaki Sanata Yariman Bakura ya shaidawa ‘Yan jarida cewa maganar sauyin-shekar ta yi nisa, kuma gwamnan ya na daf da barin PDP. Yarima ya ce: “Kwanan nan zai shigo APC.”

Wani daga cikin ‘Yan APC, Alhaji Abdullahi Abubakar Tsafe, wanda shi ne Kwamishinan raya karkara a Zamfara, ya na cikin wadanda su ke fitowa su na kira ga gwamnan ya koma APC.

KU KARANTA: Gwamnan Oyo Seyi Makinde ya warke daga cutar Coronavirus

Ana neman Gwamna Matawalle ya koma Jam’iyyar APC a Zamfara

Bello Matawalle ya zama Gwamna a Zamfara bayan hukuncin kotu
Source: UGC

Abdullahi Abubakar Tsafe ya na cikin Yaran bangaren Kabiru Garba Marafa a jam’iyyar APC. Bello Matawalle ya tafi da wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar hamayya a cikin gwamnatinsa.

Tsafe ya yabawa aikin sabon gwamnan inda ya ke cewa tsohon gwamna Abdulaziz Yari ya gaza yin abin da gwamnatin Matawalle ta yi, duk ya samu damar yin shekaru takwas a mulki.

Wani daga cikin ‘Ya ‘yan APC ya soki wannan kira, ya bayyana cewa Zamfara ta na cikin inda aka biznewa APC cibiya. Jagoran ya zargi masu wannan kira da neman cin gumin wasu.

Mataimakin shugaban APC a Zamfara, Alhaji Sani Gwamna Mayanchi, ya ce babu wani dalilin da zai sa mutane su rika fitowa su na kiran gwamna Bello Matawalle ya dawo tafiyar APC.

Sani Gwamna Mayanchi wanda ya ke tare da bangaren Abdulaziz Yari ya bayyana cewa uwar jma’iyya ba ta san da zaman Sanata Kabiru Marafa a matsayin shugabanta a jihar Zamfara ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel