Ba Ma’aikacinmu ba ne ya ke dauke da kwayar cutar COVID-19 – Inji NNPC

Ba Ma’aikacinmu ba ne ya ke dauke da kwayar cutar COVID-19 – Inji NNPC

Kawo yanzu akwai mutane fiye da 200 da aka tabattar cewa sun kamu da cutar Coronavirus a Najeriya. Yanzu haka mun ji cewa wannan cuta ta shiga gidajen ma'aikatan NNPC.

Kamfanin NNPC ta tabbatar da cewa an samu wani Bawan Allah da ke dauke da wannan cuta ta COVID-19 a gidajen Ma’aikatan kamfanin man da ke Unguwar Garki a Birnin Abuja.

Shugaban jami’in hulda da Manema labarai na kamfanin NNPC, Dr. Kennie Obateru, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a babban birnin tarayya Abuja a jiya Ranar Asabar.

Dr. Kennie Obateru ya musanya rade-radin cewa cutar ta barke a Unguwar gidajen ma’aikatan na NNPC. Jami’in kamfanin ya ce wanda ya kamu da cutar ba ma Ma’aikaicinsu ba ne.

A cewar Kennie Obateru wanda aka samu ya na dauke da wannan cuta wani Bawan Allah ne da yawo daga kasar Ingila a cikin ‘yan kwanakin nan bayan cutar ta barke a Birtaniya.

KU KARANTA: Najeriya ba za ta rika bada gawar wadanda COVID-19 ta kashe ba

Ba Ma’aikacinmu ba ne ya ke dauke da kwayar cutar COVID-19 – Inji NNPC
NNPC ta ce wanda ya ke dauke da COVID-19 ba Ma'aikacin ta ba ne
Asali: UGC

Jawabin na Obateru ya ke cewa: “Mu na sane da matakan da Hukumar da ke kula da yaduwar cututtuka a Najeriya ta NCDC ta dauke game da wannan tilon lamari da ya auku.”

Kawo yanzu wannan matsala ba ta barkowa jama’a ba tukuna kamar yadda Jami’in kamfanin ya bayyana. “Wanda ya kamu da cutar ba ya cikin ma’aikatan kamfanin man NNPC.”

“Wani Bawan Allah ne wanda ya dawo daga Kasar Birtanyi kwanan nan ya fara nuna alamun wannan cutar. NCDC ta tabbatar da cewa ya kamu bayan da aka yi masa gwaji.”

“Kamar yadda NCDC ta tsara, an dauke duka mutanen da ke rumfarsa zuwa wani wuri inda aka killacesu, yayin da hukumar NCDC su ka yi wa wannan gida feshin cutar.” Inji sa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel