Ya kamata lantarki ta zama kyauta a lokacin annobar nan – Femi Gbajabiamilla

Ya kamata lantarki ta zama kyauta a lokacin annobar nan – Femi Gbajabiamilla

Ganin yadda Jama’a su ke ta fama da kulle da kuncin rayuwa a lokacin wannan annoba ta cutar COVID-19, majalisar wakilan tarayya ta yi kira da cewa a ba mutan wuta kyauta.

Shugaban majalisar wakilan Najeriya ta na ganin cewa akwai bukatar a dauki watanni biyu ana amfani da wutar lantarki kyauta a fadin kasar nan ba tare da an biya sisin kobo ba.

Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yi wannan kira a lokacin da shi da wasu shugabannin majalisar tarayya su ka gana da wasu kusoshi da manya na gwamnatin shugaban kasa Buhari.

Daga cikin wadanda su ka zauna da shugabannin majalisar kasar akwai Ministar tattalin arziki da kasafi, Zainab Ahmad Shamsuna da kuma Darektan ofishin kasafi, Ben Akabueze.

Kamar yadda mu ka samu labari, shugaban majalisar wakilan ya yi magana game da sha’anin lantarki da kuma kudin da gwamnati ta ke neman batarwa domin bunkasa tattali.

KU KARANTA: Ana neman Majalisa ta amince a kafa asusun tallafin COVID-19

Ya kamata lantarki ta zama kyauta a lokacin annobar nan – Femi Gbajabiamilla
Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya na so a dakatar da karbar kudin wutan lantarki
Asali: UGC

Hadimin kakakin majalisar wanda ke taimaka masa wajen hulda da Manema labarai, Lanre Lasisi, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a madadin Mai gidansa a jiya.

Rt. Hon. Gbajabiamila ya ce akwai bukatar a tashi tsaye wajen ganin bayan wannan cuta. Gbajabiamila ya ce yadda jama’a su ke kunshe a gida, lantarki zai yi masa amfani.

Gbajabiamila ya bayyana cewa majalisa za ta duba rokon da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke yi na ba shi damar narka wasu kudi domin ceto tattalin kasar a marrar nan.

A wannan zama an kuma cin ma matsaya cewa za a bude majalisar tarayyar a Ranar 14 ga Watan Afrilun 2020. ‘Yan majalisar za su yi biyayya ga wa’adin da gwamnatin tarayya ta sa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel