Wata mata ta sadaukar da kudinta na tafiya aikin Hajji don a yaki cutar Coronavirus

Wata mata ta sadaukar da kudinta na tafiya aikin Hajji don a yaki cutar Coronavirus

- Wata tsohuwar mata musulma daga yankin Jammu da Kashmir ta yi abinda ya matukar ba wa jama'a mamaki

- Tsohuwar matar ta yi amfani da makuden kudadenta da ta dinga tarawa don zuwa Saudi Arabia sauke farali, wajen sadaka

- Matar ta yi hakan ne bayan ganin mummunan halin da mutane suka fada sakamakon barkewar annobar coronavirus

Wata mata musulma daga Jammu da Kashmir ta bada sadakar kudin da ta dinga tarawa don zuwa aikin hajji. Jimillar kudin ya kai Rs. 500,000 don yakar cutar coronavirus.

Khalida Begum mai shekaru 87 ta adana makuden kudaden ne don shirin tafiya aikin hajji da take yi a 2020. Ta kuwa sadaukar da kudin ne don tallafi ga jama'a sakamakon barkewar muguwar cutar coronavirus. Sakamakon rufe kasar Saudi Arabia da aka yi, ta canza tsarinta inda ta yanke hukuncin bada sadakar dukkan kudin.

Wata mata ta sadaukar da kudinta na tafiya aikin Hajji don a yaki cutar Coronavirus
Wata mata ta sadaukar da kudinta na tafiya aikin Hajji don a yaki cutar Coronavirus
Asali: Facebook

Hajji babban al'amari ce a rayuwar kowanne musulmi.

Khalida Begum ta ga jama'a masu yawa na fama ne sakamakon barkewar muguwar cutar a duniya. A don haka ne ta yanke hukuncin sadaukar da tafiya hajjinta don tallafar rayuwar jama'a.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Tabin hankali na daya daga cikin sabuwar alamar kamuwa da Coronavirus

Khalida Begum na daya daga cikin mata kalilan na yankin Jammu da Kashmir da suka samu damar yin karatu a makarantar turawa duk da cewa ana kisan gilla ga musulmai a Kashmir.

Sirika ce ga Kanal Peer Mohd Khan wanda shine shugaban Jana Sangh.

Masu rajin kare hakkin bil Adama sun jinjinawa kokarinta. Sun kara da cewa duk da shekarunta, ba ta dena taimako ga jama'a ba da walwalar mata a Indiya.

Hakazalika, dan ta Farooq Khan ne mai bada shawara ga Laftanal Gwamnan Jammu da Kashmir.

Haka kuma Likitocin kwakwalwa na duniya sun ce kadan daga cikin wadanda suka kamu da muguwar cutar a kasashe masu tasowa na samun tabin kwakwalwa.

Duk da zazzabi, tari da kuma wahala wajen numfashi suna daga cikin alamomin kamuwa da cutar coronavirus, wasu majinyatan sun nuna wasu alamu na tabuwar kwakwalwa.

Wadannan alamun sun hada da rashin tantance wari ko kamshi tare da ciwo na zuciya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel