COVID: Nur Husseini ya mutu a Landan, Jaririn mako 6 ya kwanta dama a USA
Tsohon shugaban kasar Somaliya, Nur Hussein ya rasu bayan ya yi fama da cutar COVID-19. Husseini ya rasu ne a Ranar Laraba, 1 ga Watan Afrilu, 2020 a kasar Ingila.
Kamar yadda labari ya zo mana, Nur Hussein ya cika ne a asibitin Makarantar King’s College da ke birnin Landan. Marigayi Hussein ya bar Duniya ne ya na da shekaru 83.
Iyalin tsohon shugaban ne su ka sanar da rasuwarsa. Yanzu haka ana makokin wannan Bawan Allah da ya rike kujerar Firayim Minista a Somaliya tsakanin 2007 da 2009.
A can kasar Ingilar dai, babban ‘Dan wasan damben Duniya mai tashe, Anthony Joshua ya bayyana cewa ya rasa wasu na kusa da shi a sakamakon barkewar cutar.
A jiya Laraba, Anthony Joshua ya fito ya na cewa: “Ban rasa wani na kut-da-kut ba, amma na rasa na kusa da ni a wajen aiki, da kuma Abokai da Abokan wasu Abokai na”
KU KARANTA: China ba ta fadar gaskiyar mutanen da COVID-19 ta kashe
‘Dan wasan ya yi kira ga jama’a da su yi ta-ka-tsan-tsan da wannan muguwar cuta. A cewarsa barnar COVID-19 ta na kara kamari yayin da cutar da ta ke cigaba da yaduwa.
Idan mu ka tafi kasar Amurka a wata Nahiyar, za mu ji labarin cewa cutar COVID-19 ta ga bayan wani yaro mai makonni shida rak a Duniya. Jaririn ya mutu ne a jiya Laraba.
Gwamnan jihar Connecticut, Ned Lamont, ya bayyana wannan a shafinsa na Tuwita. Gwamna Lamont ya bayyana cewa Jaririn da aka kawo asibiti a makon jiya ya mutu.
Bayan an yi gwaji, an tabbatar da cewa Jaririn ya kamu da COVID-19. Lamont ya yi jimamin wannan rashi wanda ya na cikin mafi kankantar da cutar ta kashe a Duniya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng