Jami’an yan sanda karkashin jagorancin DPO sun yiwa wani matashi duka har lahira a Abuja

Jami’an yan sanda karkashin jagorancin DPO sun yiwa wani matashi duka har lahira a Abuja

- Jami'an yan sanda a yankin Abaji sun ci zarafin wani matashi har lahira

- An tattaro cewa yan sandan karkashin jagorancin DPO ne suka lallasa matashin da abokansa

- Sai dai DPO din ya karyata zargin cewa sune suka halaka matashin

Wani rahoto daga jaridar Daily Trust ya nuna cewa matasa a yankin Abaji da ke Abuja sun yi zanga-zanga a kan mutuwar wani dan shekara 25, Saidu Babale, wanda ake zargin yan sanda sun yiwa duka har lahira.

Wani mazaunin yankin da abun ya faru a kan idonsa, Abdullahi Kabiru, ya bayyana cewa lamarin ya afku ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris da misalin karfe 12:30 na dare lokacin da wasu matasa ciki harda marigayin, suka kange hanya don hana yan sanda karkashin jagorancin DPO, CSP Umar Musa wucewa ta unguwar.

Ya ce matasan wadanda ke bacci a waje kusa da hanyar sakamakon zafi da ake, sun hangi motar yan sandan na zuwa Sannan suka tashi suka yi amfani da benci wajen kewaye hanyar.

Jami’an yan sanda karkashin jagorancin DPO sun yiwa wani matashi duka har lahira a Abuja
Jami’an yan sanda karkashin jagorancin DPO sun yiwa wani matashi duka har lahira a Abuja
Asali: Facebook

A cewarsa sai DPO din da jami’ansa suka fito daga motar Sannan suka cire shingen amma sai fusatattun matasan suka dunga jifan DPO din da jami’ansa da duwatsu yayinda suka tsere.

“Washegari sai DPO din ya umurci da a bi matasan da suka jefe su. An gano su sannan aka kama su. Aka kuma kai su ofishin yan sanda,” in ji shi.

An yi zargin cewa yan sanda sun lallasa matasan inda daya daga cikinsu ya shiga mawuyacin hali Inda aka kwashe shi zuwa asibiti inda ya mutu daga bisani.

An tattaro cewa mutuwar nasa ne ya sa wasu matasa a yankin yin zanga-zanga.

Wani yayan marigayin, Abubakar Sadiq Yahaya, ya ce ahlinsu za su nemi hakkin kashe masa dan uwa da aka yi.

Ya ce ya shiga alhini a lokacin da wata motar Golf ta kowo dan uwansa gida a safiyar ranar Juma’a 27 ga watan Maris.

A cewarsa jikin dan uwan nasa ya yi kaca-kaca a cikin jini a lokacin da aka kawo sa.

Ya ce da aka tambayi direban daga inda ya samo shi, sai direban ya ce ofishin yan sandan Abaji ne suka ce ya kawo shi gida.

Hakazalika wani Ahmed Abdulkarim wanda aka kama tare da marigayin ya ce tare yan sanda suka yi masu dukan tsiya.

Ya yi zargin cewa yan sandan sun lallasa su a cikin wajen ajiye masu laifi, cewa yan sandan sun daure masu hannu da kafa Sannan suka dunga dukansu da kulki.

Abdulkarim ya kuma ce DPO din baya nan a lokacin da aka fara dukansu amma da ya dawo sai yace a kara masu hukunci.

KU KARANTA KUMA: Tun dama chan rabin albashi Buhari da Osinbajo suke karba – Adesina

Da yake martani kan zargin, DPO, CSP Musa, ya karyata cewar su suka lallasa marigayin.

Ya ce ya ziyarci asibiti domin sanin halin da matasan uku ke ciki inda aka gaya masa cewa daya daga cikinsu ya mutu, cewa daga yan banga da suka kawo su ofishin yan sanda da daga cikin jami’ansa sun rubuta jawabi kuma an mika shi ga ofishin CID don ci gaba da bincike.

A wani labari na daban, mun ji cewa Shagunan saye da sayarwa da ke cikin unguwanni da gefen hanya za su iya cigaba da harkokinsu na kasuwanci matukar sun girmama dokar nesanta da taron jama'a da suka wuce 20, kamar yadda rundunar 'yan sandan jihar Legas ta bayyana ranar Lahadi.

Rundunar 'yan sandan ta bayyana hakan ne a matsayin martani a kan rahoton da ta samu a kan cewa masu kananan shaguna da ba a cikin kasuwa suke ba sun fara daina bude shagunansu domin yin biyayya ga dokar rufe kasuwanni da walwalar jama'a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel