Tun dama chan rabin albashi Buhari da Osinbajo suke karba – Adesina

Tun dama chan rabin albashi Buhari da Osinbajo suke karba – Adesina

- Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa tun dama chan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo na karban rabin albashinsu ne duk wata

- Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ne y bayyana hakan a yayinda yake martani ga sadaukar da rabin albashi da yan majalisa suka yi

- Adesina ya yi bayannin cewa dukkanin shugabannin biyu sun zabi karban rabin albashinsu tun da gwamnati mai ci ta karbi mulki a 2015

Rahotanni sun kawo cewa tun kafin barkewar annobar Covid-19 wanda aka fi sani da coronavirus, dama chan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo na karban rabin albashinsu ne duk wata.

Mai ba Shugaban kasa shawara na musamman a kafofin watsa labarai, Mista Femi Adesina ne ya bayyana hakan a wata hira da Channels TV a shirin Politics Today.

Tun dama chan rabin albashi Buhari da Osinbajo suke karba – Adesina

Tun dama chan rabin albashi Buhari da Osinbajo suke karba – Adesina
Source: UGC

“Tuni dama Shugaban kasa da mataimakin Shugaban kasa ke karban kaso 50 na albashinsu, basa karban kaso 100,” ya bayyana a ranar Talata, 31 ga watan Maris.

Adesina ya yi bayannin cewa dukkanin shugabannin biyu sun zabi karban rabin albashinsu tun da gwamnati mai ci ta karbi mulki a 2015.

Koda dai bai bayyana abunda ake yi da rabin albashin nasu ba tsawon shekarun, ya yarda cewar shugabannin biyu sun yi bajinta sannan kuma za su bayar da tallafi domin magance coronavirus a ra’ayin kansu.

Da aka tambaye shi ko Shugaban kasar da mataimakinsa za su bayar da albashinsu kamar yadda yan majalisar dattawa da na majalisar wakilai suka yi, ya ce: “Ba zan iya tabbatar da hakan ba; mambobin majalisar zartarwa za su bayar da kaso 50 na albashinsu na watan Maris.”

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Najeriya ta rasa wani babban likitanta da ke kula da marasa lafiya a Ingila

“Tuni dama, Shugaban kasa da mataimakinsa ke karban kaso 50. Tun daga farkon mulkinsu, sun zabi karban rabin albashin da ya kamata su karba...neman su sake yin wani abu zai zamo a ra’ayin kansu,” in ji hadimin Shugaban kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel