Coronavirus: Yadda titunan Abuja suka zama tamkar kufai (hotuna)

Coronavirus: Yadda titunan Abuja suka zama tamkar kufai (hotuna)

A yayinda aka sanya dokar hana fita a wasu yankunan kasar a kokarin da ake na hana yaduwar cutar coronavirus, an gano titunan Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya sun zama tamkar kufai, inda ko ina ya zama wayam babu mutane.

Hakan ta kasance ne a ranar Talata,31 ga watan Maris, bayan dokar da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanya ta hana fita ta soma aiki.

A jawabin da shugaba Buhari ya yi a karshen makon da ya gabata, ya umarci a rufe biranen Abuja, Lagos da kuma Ogun na tsawon mako biyu a wani matakin hana yaduwar coronavirus.

Ya zuwa yanzu dai mutum 131 ne suka kamu da cutar a Najeriya, 25 daga cikinsu a Abuja ne.

Ga hotunan yadda birnin tarayyar ta koma a kasa:

Coronavirus: Yadda titunan Abuja suka zama tamkar kufai (hotuna)
Coronavirus: Yadda titunan Abuja suka zama tamkar kufai (hotuna)
Asali: Twitter

Coronavirus: Yadda titunan Abuja suka zama tamkar kufai (hotuna)
Coronavirus: Yadda titunan Abuja suka zama tamkar kufai

KU KARANTA KUMA: Coronavirus ta kashe tsohon shugaban kasar Congo

A halin da ake ciki, mun ji cewa Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a daren jiya Litinin ya saka hannu kan wata doka ta ayyana Covid-19 a matsayin annoba mai hatsari a duniya.

Sanarwar ta mai bawa shugaban kasar shawara na musamman kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina ya fitar ta ce shugaban kasar ya yi amfani da ikon da kudin tsari mulki ta bashi a sashi na 2,3 da 4 na Quarantine Act (CAP Q2 LFN 2004) ya rattaba hannu a kan dokar Covid-19 a ranar Litinin.

Dokar da za ta fara aiki daga ranar 30 ga watan Maris na 2020 za ta bawa gwamnati izinin aiwatar da mafi yawancin matakan da shugaban kasa ya lissafa a jawabin da ya yi wa 'yan kasa a ranar 29 ga watan Maris na 2020 da suka hada da Takaita ko hana zirga-zirga a Legas, Abuja da Ogun a matsayin mataki na takaita yaduwar annobar a kasar.

Kazalika, dokar ta bawa bankuna da wasu hukumomi masu hada-hada da kudade damar yin harkokinsu ta intanet wato yanar gizo da saka kudade a na'uarorin ATM da abokan huldarsu za su rika amfani da shi duk da dokokin da aka saka a kasar na takaita ayyuka da hada-hada a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel