COVID-19: Kasar Amurka za ta dauke mutanen ta daga Najeriya

COVID-19: Kasar Amurka za ta dauke mutanen ta daga Najeriya

Mun samu labari cewa Amurkan da ke cikin Najeriya za su koma kasarsu. Ofishin Jakdancin Amurka da ke Legas ya shaidawa Duniya haka a farkon makon nan.

Kasar Amurka ta tanadi jiragen sama na musamman da za su dauke mutanenta daga Najeriya. Kasar ta dauki wannan mataki ne sabili da barkewar COVID-19.

Jawabin ya nuna cewa jiragen saman za su tashi kai-tsaye ne daga babban filin sauka da tashin jiragen saman Najeriya na Murtala Muhammed da ke Garin Legas.

Jakadancin kasar ta Amurka ta fitar da wannan bayani a shafinta na yanar gizo. Amurka ta ce ta na kokarin kai wani jirgin filin Nnamdi Azikiwe da ke Garin Abuja.

Hukumomin na Amurka sun fadawa mutanensu cewa su tafi filin jirgi da zarar sun samu wasikar da ke tabbatar da cewa sun samu wuri a jirgin saman da zai dauke su.

KU KARANTA: An gurfanar da wadanda su ka jagoranci sallah a lokacin annoba

COVID-19: Kasar Amurka za ta dauke mutanen ta daga Najeriya

Mutanen Kasar Amurka da ke zaune a Najeriya za su koma gida
Source: Depositphotos

Har ila yau, wannan jawabi da ofishin Jakadancin Amurka ta yi, ya nuna cewa ba za a bar wadanda ba su samu wannan takarda su shiga filin jirgin saman ba.

Jiragen za su tashi ne daga Garin Ikeja zuwa babban filin jirgin saman nan na Washington-Dulles da ke Garin Virginia a cikin babban birnin Amurka na Washington DC.

Ana sa ran wannan jirgi zai isa Amurka a cikin makon nan bayan ya dauki ‘Yan kasar. A jiya mu ka ji cewa za a dauke ‘Yan kasar Israila da ke zaune a cikin Najeriya.

A halin yanzu dai babu kasar da ta ke da yawan wadanda su ka kamu da cutar Coronavirus kamar Amurka. Akwai mutane kusan 140, 000 da ke da cutar a Amurka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel