Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu yan kasar China su 2 a Ebonyi

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu yan kasar China su 2 a Ebonyi

- Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da wasu yan kasar China su biyu

- An tattaro cewa an sace mutanen ne a karamar hukumar Ivo da ke jahar

- Rundunar yan sanda ta tabbatar da lamarin yayinda ta ba da tabbacin ceto su ba tare da bata lokaci ba

Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da wasu yan kasar China su biyu da ke aiki a jahar Ebonyi a ranar Litinin, 30 ga watan Maris.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an yi garkuwa da mutanen ne a yankin karamar hukumar Ivo da ke jahar.

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu yan kasar China su 2 a Ebonyi

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu yan kasar China su 2 a Ebonyi
Source: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa wadanda aka sacen sun kasance masu aiki a wani kamfanin sarrafa ma’adinai a yankin.

An tattaro cewa kwamishinan yan sandan jahar Ebonyi, Awosola Awotide ya tabbatar da lamarin.

Ya bayar da tabbacin ceto mutanen biyu ba tare da jimawa ba, inda ya ce rundunar ta bi sahun masu garkuwan.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Sakamakon gwaji ya nuna mutane 5 da ake zargin sun kamu a Borno basa dauke da cutar

A wani labarin kuma mun ji cewa dakarun rundunar Sojin Najeriya dake aikin Operation Hadarin Daji sun ceto mutane 12 daga hannun masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Bungudu ta jahar Zamfara, daga cikinsu har da hakimin Wuya.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito mukaddashin daraktan watsa labaru na hukumar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Benard Onyeuko ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 29 ga watan Maris, inda yace Sojojin sun kama yan bindiga 9, sun kama 14 a Zamfara.

Birgediya Onyeuko ya bayyana cewa Sojoji sun banka wuta a gidaje 13 mallakin gungun yan bindiga daban daban a garuruwan Gidan Usman, Gidan Babagoji, Gadauna, Gidan Janari, Kekuwa, Gidan Sarki, Gardi da Binhgi.

“Dakarun Operation Hadarin Daji a jahar Zamfara sun halaka yan bindiga da dama a makon da ta gabata, tare da kubutar da mutane 12 da aka yi garkuwa da su, daga cikinsu har da hakimin Wuya, wanda aka yi garkuwa da shi a makon da ta gabata.

“Haka zalika a yayin samamen da Sojoji suka kai a garuruwan Gidan Usman, Gidan Babagoji, Gadauna, Gidan Janari, Kekuwa, Gidan Sarki, Gardi da Bingi, duk a cikin karamar hukumar Bungudu na jahar Zamfara, sun kashe yan bindiga 9, sun kama 14, kuma sun kona gidaje 13. Bugu da kari Sojoji sun kwato shanu 67, kuma tuni suka mikasu ga hakiman yankin.” Inji shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel