An shiga rudani da juyayi a majalisar Kaduna tun bayan da El-Rufai ya kamu da coronavirus

An shiga rudani da juyayi a majalisar Kaduna tun bayan da El-Rufai ya kamu da coronavirus

Rahotanni sun kawo cewa yan majalisar dokokin jahar Kaduna sun shiga alhini da rudani sakamakon sanarwar da Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya yi a ranar Asabar, na cewar sakamakon gwaji ya nuna yana dauke da cutar Coronavirus.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sanarwar da El-Rufai ya yi ya sanya fargaba a zukatan wasu yan majalisa musamman wadanda suka yi aiki dab da dab dashi a makon da ya gabata, domin basu na san ya yi gwajin ba.

Masu koro jawabi daga gidan Sir Kashim Ibrahim sun bayyana cewa wasu mambobin majalisar ma sun shiga killace kansu tun bayar sanarwar, yayinda Shugaban ma’aikatan gwamnan, Mohammed Sani Dattijo wanda kan kasance tare dashi a koda yaushe ya yi gwaji kuma sakamako ya nuna baya dauke da cutar.

An shiga rudani da juyayi a majalisar Kaduna tun bayan da El-Rufai ya kamu da coronavirus

An shiga rudani da juyayi a majalisar Kaduna tun bayan da El-Rufai ya kamu da coronavirus
Source: UGC

Uwargidar gwamnan, Hajiya Hadiza Isma El-Rufai ma ta je shafin ta na Twitter inda ta bayyana cewa za a kai samfirin jininta gwaji a ranar Lahadi sannan ta yi godiya ga yan Najeriya kan addu’o’insu da fatan alkhairi da suka yiwa gwamnan.

Akwai rahotannin cewa mataimakiyar gwamnan jahar, Dr. Hadiza Balarabe da sakataren gwamnatin jahar, Balarabe Lawal Abbas ma sun yi gwajin.

Sai dai an tattaro cewa tun bayan sanarwar wasu kwamishinoni da hadimansu sun shiga damuwa inda daya daga cikin kwamishinonin ya bayyana cewa koda dai bai haduda gwamnan ba tsawon makonni biyu da suka gabata, ya hadu da manyan jami’an gwamnati wadanda suka hadu da gwamnan.

KU KARANTA KUMA: Ka bani naira biliyan 1 domin na yaki Coronavirus – Gwamnan Anambra ga Buhari

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa koda dai gwamnan bai yi tafiya zuwa wajen kasar ba a wata guda da ya gabata kuma bai halarci taron gwamnonin APC da shugaban kasa Buhari ba a ranar 16 ga watan Maris, ya kasance a taron majalisar tattalin arziki a Abuja a ranar 19 ya watan Maris inda ya hadu da gwamnonin jiha ciki harda Bala Mohammed na jahar Bauchi wanda ke dauke da cutar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel