An tabbatar da samun kwayar cutar coronavirus a jikin sojoji biyu a Maiduguri

An tabbatar da samun kwayar cutar coronavirus a jikin sojoji biyu a Maiduguri

Dakarun Sojin Najeriya biyu ne aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar coronavirus bayan gwajin da aka yi musu a Monguno, jihar Borno, kamar yadda jaridar Sahara reporters ta tabbatar a rahoton da ta wallafa da yammacin ranar Lahadi.

Sojojin biyu da suka dawo sansaninsu bayan sun dawo daga hutu, an killacesu ne a sashi na uku na hedkwatarsu don lura dasu tun ranar Asabar, 28 ga watan Maris, 2020.

Ba a tabbatar da cewa ko hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta hada da sojojin ba a cikin jimillar wadanda aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar a kasar nan ba.

Tun farkon samun bullar kwayar cutar coronavirus a Najeriya ta hannun wani dan kasar Italiya, an tabbatar da samun kwayar cutar a jihohin Najeriya 12.

An tabbatar da samun kwayar cutar coronavirus a jikin sojoji biyu a Maiduguri

An tabbatar da samun kwayar cutar coronavirus a jikin sojoji biyu a Maiduguri
Source: Twitter

Ya zuwa yanzu kwayar cutar coronavirus ta hallaka mutane 15,000 a fadin duniya.

DUBA WANNAN: COVID-19: abinda Dangote ya fada bayan sakamakon gwajinsa ya fito

Mutum daya ne ya mutu a Najeriya bayan kamuwa da kwayar cutar coronavirus, amma adadin masu dauke da cutar ya kai mutum 96, kamar yadda kididdigar cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta nuna.

Ga jerin jihohin Najeriya da aka tabbatar da samun kwayar cutar coronavirus da adadin mutanen da suka kamu da ita;

1. Legas - mutum 59

2. Abuja - mutum 16

3. Ogun - mutum 3

4. Ekiti - mutum 1

5. Edo - mutum 2

6. Bauchi - mutum 2

7. Enugu - mutum 2

8. Oyo - mutum 7

9. Benue - mutum 1

10. Kaduna - mutum 1

11. Ribas - mutum 1

12. Osun - mutum 2

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel