Saudiyya ta sanar da warkewar mutum 66 da suka kamu da kwayar cutar COVID-19 (bidiyo)
A ranar Lahadi ne hukumar kasar Saudi Arabia ta sanar da cewa wasu mutane 66 da suka kamu da kwayar cutar coronavirus sun warke.
Sanarwar na kunshe ne a cikin sakon da babbar jaridar kasar Saudiyya da ake wallafa wa cikin harshen turanci; 'Saudi Gazette' ta fitar ranar Lahadi.
Akwai kimanin mutum 96 da aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayar cutar coronavirus a kasar Saudiyya tare da asarar rayukan mutane 8.
Ya zuwa yanzu, kwayar cutar coronavirus ta kashe mutane fiye da 30,000 a fadin duniya a karshen makon nan. Kwayar cutar ta fi gigita kasar Amurka da yankin nahiyar turai a 'yan kwanakin baya bayan nan.
A ranar Lahadi ne kasar Andolus (Spain) ta sanar da mutuwar mutane 838 sakamakon kamuwa da kwayar cutar coronavirus.
DUBA WANNAN: Jerin jihohin Najeriya 12 da aka tabbatar da bullar kwayar cutar coronavirus
A wata kididdiga da jami'ar 'Johns Hopkins' ta gudanar, ta bayyana cewa mutane 30,800 ne kwayar cutar COVID-19 ta halllaka a fadin duniya, yayin da take cigaba da mamaya da karya tattalin arzikin mutane da na kasashe.
Mutane fiye da 20,000 ne kwayar cutar ta hallaka a iya yankin nahiyar turai. Kwayar cutar ta kashe mutane fiye da 1400 a rana daya a kasar Spain da Italy.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng