Rawar da coronavirus za ta taka a shari'ar da Dino ya shigar da Adeyemi

Rawar da coronavirus za ta taka a shari'ar da Dino ya shigar da Adeyemi

Rahotanni sun kawo cewa an shiga halin fargabar cewar annobar coronavirus na iya shafar harkokin zaman shari’ar kotun zaben sanata na yankin Kogi ta yamma wanda za a yi a Abuja, babbar birnin tarayar kasar.

Sanata Dino Melaye, wanda ya yi takarar kujerar sanata a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), na kalubalantar nasarar Sanata Smart Adeyemi na jam’iyyar All Progressives Congress’ (APC) a zaben shekarar da ya gabata.

Koda dai maalisar shari’a ta kasa ta yi umurnin tsayar da harkokin kotuna, hakan bai shafi kotunan zabe ba saboda kundin tsarin mulki ta kafa su ne akan wasu wa’adi.

Za a dawo zaman sauraron shari’ar ne a gobe Litinin, 30 ga watan Maris.

Rawar da coronavirus za ta taka a shari'ar da Dino ya shigar da Adeyemi
Rawar da coronavirus za ta taka a shari'ar da Dino ya shigar da Adeyemi
Asali: UGC

Dino da shaidun PDP sun bayar da shaida a gaban kotun zaben karkashin jagorancin Justis Kahim Kaigama, kafin yaduwar mummunan annobar.

Sai dai kuma, majiyoyi daga APC sun ce tsoro ya cika zukatan shugabannin jam’iyyar game da lafiyar shaidun da za a kwasa daga jahar Kogi zuwa Abuja a wannan lokaci mai wuyar sha’ani.

KU KARANTA KUMA: Sakamakon gwaji ya nuna gwamnan Neja baya dauke da cutar coronavirus

Hakazalika, an tattaro cewa sanatan na APC, wanda ke ganin yana da kwakkwaran yancin lashe shari’an, ya shiga zullumi kan yadda za ta kasance idan suka ki bayyana a kotu ko kuma karancin shaidu da za su hallara a kotun zaben a Abuja.

A wani labari na daban, mun ji cewa shugaban asibitin da ke jami’ar Ibadan, Farfesa Jesse A Otegbayo ya tabbatar da cewa ya kamu da cutar Coronavirus a halin yanzu. Jesse A Otegbayo ya bada wannan sanarwa ne a wani jawabi da ya fitar da hannunsa.

Jesse A Otegbayo ya kamu da wannan cuta ne a taron da su ka yi kwanaki. Farfesa Otegbayo ya ce bayan sun fara gudanar da wani taro na shugabannin asibitin UCH a makon jiya, sai su ka fahimci Abokin aikinsu ya kamu da COVID-19.

Otegbayo ya shaidawa ‘Yan jarida cewa wannan ya sa su ka dakatar da taron, sannan kuma aka yi wa wannan Bawan Allah gwaji, inda aka tabbatar ya kamu da cutar.

A dalilin haka, Jesse A Otegbayo da sauran Likitoci su ka killace kansu, sannan aka yi masu gwaji. Bayan sakamako ya fita, an gane cewa cutar ta kama Likitan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel