Amurka za ta janye mutanen ta baki daya daga Najeriya saboda annobar Coronavirus
Gwamnatin kasar Amurka ta bayyana shirinta na janye duka mutanen ta baki daya daga Najeriya duk kuwa da rufe tashi da saukar jiragen sama da gwamnatin kasar tayi
Ofishin jakadancin Amurka na Najeriya ne ya bayyana haka jiya Juma'a da yamma.
A sanarwar da ofishin ya fitar, ya bayyana cewa, ana so duka 'yan kasar Amurka da suke Najeriya da su hallara a birnin Abuja ko Lagos, domin su samu damar bin jirgin sama da kasar ta Amurka za ta aiko. Haka kuma ta shawarci mutanen da basa biranen Abuja da Lagos din da su gaggauta bin jirgi da zai kai su biranen guda biyu kafin lokacin da kasar ta Amurka za ta gama shirye-shiryen nata.
KU KARANTA: Mata ta kashe mijinta da wuka kan zargin yana lalata da wata a titi
Ta ce: "A yanzu haka babu wani jirgi da yake zuwa kasar Amurka, amma muna bakin kokarin mu wajen samar da jirgin sama da zai dauke mutanen mu duk kuwa da cewa kowacce kasa ta hana tashi da saukar jirage da shige da fice.
"Zamu aikawa da mutanen mu sako ta adireshin Email da zarar mun samu jirgin da zai dauke su.
"Yan kasar Amurka da suke da burin komawa kasarsu, ana bukatarsu da su gaggauta zuwa birnin Abuja ko Lagos.
A yanzu haka dai kasar Amurka tana dauke da mutane mafi yawa a duniya da suke da cutar Coronavirus, inda yawan su ya kai kimanin mutane dubu tamanin da shida (86,000).
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng