Amurka ta fi China yawan wadanda suka kamu da coronavirus

Amurka ta fi China yawan wadanda suka kamu da coronavirus

Rahotanni sun kawo cewa a yanzu kasar Amurka ta yi wa China zarra wajen yawan mutanen da suka kamu da cutar cornavirus.

An tattaro cewa zuwa yanzu yawan wadanda suka kamu da cutar a Amurka ya kai 85,500, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

Wasu sabbin alkaluma da jami’ar Johns Hopkins University ta tattara sun nuna Amurkar ta wuce China da kimanin 4000.

Amurka ta fi China yawan wadanda suka kamu da coronavirus

Amurka ta fi China yawan wadanda suka kamu da coronavirus
Source: Facebook

China dai na da wadanda suka kamu da cutar 81,782, inda a baya Italiya take rufe mata baya da 80,589.

To sai dai har kawo yanzu, China da Italiya na gaba da Amurkar wajen yawan wadanda suka mutu sakamakon cutar ta coronavirus, inda mutum 3,291 suka mutu a China yayin da kuma 8,215 suka mutu a Italiya sannan Amurka ta rasa mutane 1,300 sakamakon wannan annoba.

Wannan karuwar yawan alkaluman na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da shugaba Donald Trump ya sanar da cewa kasar tasa ba da dadewa ba za ta yaki cutar coronavirus.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Mu sadaukar da albashinmu na watan Maris - Dan majalisar wakilai

A gefe guda, mun ji cewa Matakan hana yaduwar muguwar cutar coronavirus da gwamnatin tarayyar Najeriya ke dauka a kasar nan suna da yawa ,kuma a halin yanzu har sun kai gidajen gyaran hali.

A cikin wannan kokarin ne gwamnati ta bada umarnin cewa a saki wadanda ake kan shari'arsu amma ake garkame dasu a gidajen.

Kamar yadda ministan lamurran cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana, an yi hakan ne don hana yaduwar cutar a gidajen gyaran hali.

Aregbesola ya bada wannan umarnin ne a yayin wani taron gaggawa da ya kira a ofishinsa a Abuja a kan yadda za a hana yaduwar cutar a gidajen gyaran hali.

Bayan taron ne ministan ya fitar da takarda wacce aka mika ga manema labarai ta hannun daraktan yada labarai da hulda da jama'a, Mohammed Manga, inda ya ce wannan umarnin ya biyo bayan hukuncin kwamitin fadar shugaban kasa na yakar cutar ne.

Ya kara da cewa an dauka matakan ne don kare masu zama a gidajen gyaran halin, ma'aikatansu da kuma sauran 'yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel