Da dumi-dumi: An samu karin mutum 14 da suka kamu da coronavirus a Najeriya, sun zama 65

Da dumi-dumi: An samu karin mutum 14 da suka kamu da coronavirus a Najeriya, sun zama 65

Sabon rahoto da muke samu daga hukumar hana yaduwar cutuka ta Najeriya wato NCDC, ta bayyana cewa an sake samun karin mutane goma sha hudu da suka kamu da cutar coronavirus a kasar.

A wani jawabi da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris da daddare, hukumar ta ce mutane 12 daga cikinsu a Lagos suke yayin da sauran biyu kuma suke Abuja.

Ta kara da cewa an gano shida daga cikinsu ne a wani jirgin ruwa, uku kuma matafiya ne a tsakanin jihohin kasar, daya kuma wanda ya yi mua'amala da mutumin da aka tabbatar yana da cutar ne.

Kawo yanzu, an tabbatar da mutum 65 da suka kamu da cutar, yayin da uku suka warke sannan daya ya mutu.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Jigawa ta rufe iyakakokin ta da Bauchi, Kano da wasu jihohi biyu

A gefe guda mun ji cewa Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris, ya sanar da cewar gwajin da aka yi masa da Coronavirus ya nuna baya dauke da cutar.

Ministan ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a yayinda ya ke bayar da bayani kan abunda gwamnati ta hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ke yi domin hana yaduwar cutar.

Da yake martani ga wata tambaya kan ko shi da wasu takwarorinsa sun yi gwaji bayan rahoton cewa sun kusanci wasu mutane da ke dashi, Mohammed ya amsa tare da bayar da tabbaci.

“Na yi gwajina kuma rahoton ya fito a safiyar yau cewa bana dauke dashi kuma wannan ne dalilin da yasa nake maku jawabi a nan.

“Duk wani mamba na Majalisar Shugaban kasa ya yi gwaji, sai dai bani da ikon fada maku matsayin lafiyarsu.

“An bani nawa sakamakon kai tsaye kamar kowa,” in ji shi.

Da yake martani ga wani tambaya kan dalilin da yasa bai killace kansa ba bayan gwajin, ministan ya yi bayanincewa shi, kamar sauran takwarorinsa a majalisar, sun dauki matakin da ya kamata.

Ya ce suna bin doka na nisantan jama’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel