Covid-19: Jerin kasuwanni 17 da gwamnatin Lagas ta rufe

Covid-19: Jerin kasuwanni 17 da gwamnatin Lagas ta rufe

A bisa umurnin da ta bayar na rufe wasu kasuwanni a jahar domin hana yaduwar cutar coronavirus, gwamnatin jahar Lagas ta saki jerin sunayen kasuwanni da ta ke so a rufe.

A cewar gwamnatin jahar, wadannan kasuwanni basu siyar muhimman kayayyakin bukata na yau da kullum kamar kayayyakin abinci da magunguna sannan cewa za a rufe su daga ranar Alhamis, 26 ga watan Maris har sai illa mashaa Allah.

Covid-19: Jerin kasuwanni 17 da gwamnatin Lagas ta rufe

Covid-19: Jerin kasuwanni 17 da gwamnatin Lagas ta rufe
Source: Twitter

Wadannan kasuwanni sune;

1. GSM village, Airport road, Ikeja.

2. Kasuwar Mandilaz a Lagos island.

3. Kasuwar Oluwole a Lagos island.

4. Kasuwar Ogba.

5. Kasuwar Ladipo.

6. Kasuwar Arena oshodi.

7. Kasuwar Oshodi.

8. Kasuwar Lawason.

9. Kasuwar Kantangua.

10. Kasuwar Alaba international.

11. Kasuwar Trade fair.

12. Kasuwar Igando, Alimosho, Abule-egba.

13. Kasuwar Ebute ero.

14. Computer village, Ikeja.

15. Kasuwar Balogun a Lagos island.

16. Iyana-ipaja.

17. Kasuwar Agege.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sakamakon gwaji ya nuna Gwamna Obaseki baya dauke da coronavirus

A baya mun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya bayar da umurnin rufe kasuwannin da ke jihar banda wadanda ake sayar da kayan abinci da magunguna.

Gwamnan ya bayar da wannan umurnin ne yayin wata taron manema labarai a kan Covid-19 wato Coronavirus a ranar Talata.

Ya ce ba zai yi wu a rufe dukkan kasuwanci ba a Legas saboda irin abinda zai faru da tattalin arzikin jihar amma za a dauki dukkan matakan da suka dace domin hana yaduwar cutar.

Ya ce, "Na kuma sake zuwa a yau domin in sanar da ku halin da ake ciki game da Covid-19 a jihar Legas da kuma matakan da muke dauka domin yaki da cutar da ta jefa duniya cikin halin ha-ulai."

Gwamnan ya shawarci mazauna garin na Legas sun guji yin tafiya zuwa wasu jihohin kuma wasu da ke wasu jihohin su yi zamansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Sanwo-Olu ya ce gwamnatinsa za ta kafa kasuwar wucin gadi na sayar da abinci a makarantu.

Ya kara da cewa an bawa hukumomin tsaro da sauran hukumomin da suke da ruwa da tsaki a harkar su hukunta duk wanda aka kama yana karya dokar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel