Yan bindiga sun yi garkuwa da yayan gwamnan Bauchi

Yan bindiga sun yi garkuwa da yayan gwamnan Bauchi

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun yi garkuwa da babban yayan gwamnan jahar Bauchi, Alhaji Adamu Mohammed Duguri, a garin Bauchi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Babban hadimin gwamnan kan kafofin watsa labarai, Mukhtar Gidado, wanda ya tabbatar da lamarin a wata hira ta wayar tarho, ya ce an yi garkuwa da Alhaji Adamu wanda aka fi sani da yaya Adamu a yammacin ranar Laraba a inda ya sama hutawa da salla tare da abokai.

Gidado ya ce wadanda suka yi garkuwa da Adamu basu kira iyalansa ba har yanzu inda ya kara da cewar an sanar da jami’an tsaro.

Yan bindiga sun yi garkuwa da yayan gwamnan Bauchi

Yan bindiga sun yi garkuwa da yayan gwamnan Bauchi
Source: UGC

Da yake bayanin lamarin, wani abokin wanda aka sacen, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yan bindiga su hudu ne suka yi garkuwa da Adamu da misalin karfe 7:00 na yamma a hanyar Anguwar Zaki ida ya saba zama yana hira da abokansa.

“Muna hira ne lokacin da wasu yan bindiga su hudu suka shigo shagon sannan suka umurci Adamu shiga motarsu ta karfi da yaji kafin suka dauke shi sannan suka y harbi a sama domin tsorata mutane,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Ministoci 8 ke cikin fargaba, suna jiran sakamakon gwaji

Da aka kira shi, kakakin yan sandan jahar bai amsa kira ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

A wani labari na daban, mun ji cewa wani mai gyaran kayayyakin wutar lantarki, Victor Edem ya kashe kansa saboda matsalar da ya fama da ita na gaza gamsar da matarsa yayin kwanciya da kuma gaza yi mata ciki.

An tsinci gawar Mista Edem, mazaunin garin Okpanam kusa a Asaba a jihar Delta a daren ranar Litinin a cikin dakinsa inda a baya ya ke zaune da matarsa da dansa kafin su rabu a shekarar bara saboda matsaloli masu dangantaka da rashin karfin mazakuta.

A cewar wata majiya, Mista Edem wanda dan asalin garin Calabar ne a jihar Cross Rivers ya sanar da daya daga cikin abokansa game da matsalar da ya ke fama da ita kuma ya yi barazanar zai kashe kansa idan bai samu maganin ta ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel