A Kaduna, Kano, Ogun, Taraba, Yobe, Gwamnoni su na cigaba da zuwa ofis

A Kaduna, Kano, Ogun, Taraba, Yobe, Gwamnoni su na cigaba da zuwa ofis

Duk da cewa wasu gwamnonin Najeriya sun hadu da masu dauke da cutar COVID-19, rahotannin Daily Trust sun tabbatar da cewa har yanzu akwai gwamnonin da ke yawo a Gari.

Sai dai akwai gwamnonin da yanzu su ka rufe kansu a cikin daki sakamakon haduwa da masu wannan cuta. Gwamnonin sun yi hakan ne domin kare lafiyar daukacin al’umma.

Rahotannin sun bayyana cewa a jihar Kaduna, Mai girma gwamna Nasir El-Rufai da Mataimakiyarsa su na cigaba da zuwa taro a ofis, amma ana zama ne nesa-da-juna.

Gwamnatin Kaduna ta kuma dauki tsauraran matakai daban-daban da za su taimaka wajen yaki da cutar. Amma gwamnan ya fita zuwa wajen feshe wata kasuwa a cikin Garin.

A jihar Kano ma dai haka lamarin ya ke, gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta takaita zirga-zirga, amma an yi taron Kwamishinoni a gidan gwamnati nesa-nesa da juna.

Mai girma gwamna Alhaji Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara bai killace kansa a daki ba. Rahotanni sun bayyana cewa har gobe ya na zuwa ofis ya yi aiki a Garin Ilorin.

KU KARANTA: Gwamna Bello bai kamu da cutar COVID - 19 ba inji Gwamnatin Kogi

A Kaduna, Kano, Ogun, Taraba, Yobe, Gwamnoni su na cigaba da zuwa ofis
Akwai Gwamnonin da ke shiga jama'a duk da haduwa da masu cuta
Asali: Facebook

Jaridar ta bayyana cewa gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya jagoranci wani taro da aka yi inda ya kafa kwamitin yaki da cutar, sannan ya gana da Malamai da Sarakai.

A jihar Akwa-Ibom, mun ji cewa Udom Emmanuel ya na cigaba da zuwa ofishinsa duk da cewa wasu Takwarorinsa sun kaurcewa jama’a, amma gwamna ya na taka-tsan-tsan.

Mai girma gwamna Bello MMatawalle ya gana da manyan jami’an ‘yan sandan da ke jihar Zamfara. A jihar Borno ma dai gwamna Babagana Zulum ya cigaba da aikinsa.

A jihar Ogun, Dapo Abiodun ya ki daukar matakin killace kansa duk da bai dade daga dawowa daga Ingila ba. Haka gwamnonin Taraba da Yobe ba su fasa zuwa aikinsu ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel