Coronavirus: Manyan abubuwan da Abba Kyari ya yi a kwanaki 10 da su ka wuce

Coronavirus: Manyan abubuwan da Abba Kyari ya yi a kwanaki 10 da su ka wuce

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya, Abba Kyari, ya na cikin wadanda su ka kamu da cutar Coronavirus bayan wata tafiya da ya yi zuwa kasar Jamus.

Jaridar Daily Trust ta kawo cikakken rahoton da ke nuna duk inda Malam Abba Kyari ya ziyarta da kuma taron da ya halarta bayan dawowarsa Najeriya kwanaki.

Da farko dai Abba Kyari ya halarci daurin auren ‘Ya ‘yan Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, inda ya hadu da irinsu Aliko Dangote da manyan masu masu iko.

Haka zalika bayan nan Kyari ya halarci taron gwamnonin APC da aka yi a Ranar 16 ga Watan Maris tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa.

Gwamnoni 16 su ka halarci wannan taro sun hada: Gana Zulum, Jide Sanwo Olu, Dapo Abiodun, Godwin Obaseki, Atiku Bagudu, Abubakar Badaru da Aminu Masari.

Sauran Gwamnonin su ne Abdulrahman Abdulrazaq, Abdullahi Sule, Mohammed Sani, Simon Lalong da kuma Rotimi Akeredolu, Abdullahi Ganduje da Inuwa Yahya.

Har ila yau a wannan taro, Hadimin shugaban kasa Malam Abba Kyari ya hadu da sauran gwamnonin APC da su ka hada da Adegboyega Oyetola, Hope Uzodinma.

Kafin nan kuma Abba Kyari ya gana da shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole. Kashegari watau 17 ga Watan Maris, Kyari ya ja tawaga zuwa jihar Kogi.

KU KARANTA: Yemi Osinbajo bai kamu da cutar COVID - 19 ba - Gwaji

Coronavirus: Manyan abubuwan da Abba Kyari ya yi a kwanaki 10 da su ka wuce
Jama'a sun yi mu’amala da Abba Kyari kafin a gano da na da COVID-19
Asali: Twitter

A jihar Kogi, Jami’in ya yi wa Gwamna Yahaya Bello ta’aziyyar rashin Mahaifiyarsa a Okene. A nan ma Kyari ya na tare da Ministocin Najeriya da Hadiman Buhari.

‘Yan rakiyar Kyari sun hada da Sanata George Akume, Alhaji Lai Mohammed, Dr. Ramatu Tijjani, Zubair Dada da kuma Mai magana da yawun bakin shugaban kasa.

Bayan wannan ta’aziyya, Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar ya na halarci taron majalisar da ke ba shugaban kasa shawara a kan harkar tattalin arziki.

Wadanda su ke wajen wannan taro na PEAC sun hada da shugabanta Farfesa Doyin Salami da kuma Dr. Mohammed Sagagi, Farfesa Ode Ojowu, da Dr. Shehu Yahaya.

Sauran ‘Yan kwamitin su ne; Dr. Iyabo Masha, Farfesa Chukwuma Soludo, Dr. Bismarck Rewane da kuma Dr. Mohammed Adaya Salisu, wadanda duk sun samu zama.

A Ranar Laraba kuma Abba Kyari ya na cikin zaman FEC na Ministocin Najeriya. Kyari ya zauna ne kusa da Mataimakin shugaban kasa da kuma Sakataren Gwamnati.

Ranar Alhamis Kyari ya halarci taron kaddamar da kwamitin NHCC a karkashin Sadiya Umar Farouq. A nan ya hadu da Babagana Monguno da wasu mutane kusan 15.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel