Boko Haram: Yadda muka yi asarar zaratan sojoji 47 a harin kwanton bauna - Rundunar soji

Boko Haram: Yadda muka yi asarar zaratan sojoji 47 a harin kwanton bauna - Rundunar soji

A ranar Talata ne hedikwatar rundunar tsaro ta kasa (DHQ) ta bayyana cewa ta yi asarar zaratan dakarun soji 47, sabanin 70 da wasu rahotanni suka bayyana cewa an kashe ranar Litinin, yayin wani harin da mayakan Boko Haram suka kai wa rundunar sojoji.

Kazalika, DHQ ta bayyana cewa dakarun soji 15 ne suka samu raunuka yayin harin kwanton baunar da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kai wa sojoji a Gorgi da ke dajin Allargano a jihar Borno.

Da yake karin bayani a kan adadin dakarun sojin da suka mutu da wadanda suka samu rauni, mai kula da bangaren watsa labarai a rundunar soji da ke yaki da ta'addanci a jihar Borno, Manjo Janar Enenche, ya ce ba yayin musayar wuta da 'yan ta'adda aka kashe sojojin ba.

A cewarsa, mayakan kungiyar Boko Haram sun kai harin kwanton bauna ne a kan tawagar dakarun soji yayin da suke dauke da wasu makamai da bama-bamai, kuma fashewar bama-baman da mayakan suka harba ne ya zama sanadiyar mutuwar dakarun sojin da 'yan ta'addar da suka kai harin.

Boko Haram: Yadda muka yi asarar zaratan sojoji 47 a harin kwanton bauna - Rundunar soji
Yadda muka yi asarar zaratan sojoji 47 a harin kwanton bauna - Rundunar soji
Asali: Facebook

"Mun shiga rudani a tsakanin ranar 23 da 24 ga watan Maris, mun yi rashin dakarunmu yayin wani harin kwanton bauna da aka kai musu a lokacin da suke kan aikin cigaba da kalen burbushin mayakan kungiyar Boko Haram da aka murkushe.

DUBA WANNAN: Coronavirus: Sabon salon aiki da ministan sadarwa, Sheikh Pantami, ya bullo da shi a ofishinsa (Hotuna)

"An kai wa sojojin harin ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Buk bayan sun samu nasarar cin galaba a kan mayakan kungiyar kungiyar Boko Haram. 'Yan ta'addar sun harbi mota ta karshe a tawagar sojojin, lamarin da ya yi sanadiyar fashewa bama-baman da ke cikin motar, kuma nan take wasu dakarun soji tare da wadanda suka kai harin suka mutu," a cewarsa.

Sannan ya kara da cewa, rundunar soji ta turo wani jirgin yaki bayan fashewar bama-baman, kuma ya yi wa sauran mayakan da basu mutu ba luguden wuta a yayin da suke kokarin tserewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel