Yanzun-nan: Allah ya yiwa wata sanatar PDP rasuwa a asibitin Ingila
- Rahoto ya kawo cewa Allah ya yiwa Sanata Rose Okoji Oko daga jahar Cross River rasuwa sakamakon wani rashin lafiya da ba a bayyana ba a Asibitin Ingila
- Kafin mutuwarta, Rose Okoji Oko ta kasance shugabar kwamitin majalisar dattawa kan kasuwancida zuba jari
- Wani makusancin yar majalisar, Patrick Ikorgor Okoroji, wanda ya ce sanatar ta mutu bayan fama da dogon rashin lafiya ya tabbatar da lamarin
Labari da ke zuwa mana ya nuna cewa Allah ya yiwa wata sanata mai wakiltan yankin Cross River ta arewa, Rose Okoji Oko rasuwa.
Marigayiyar wacce ta rasu a daren jiya Litinin, 24 ga watan Maris a wani cibiyar lafiya a Ingila tana a zangonta na biyu ne a majalisar dokokin tarayya kuma ta kasance shugabar kwamitin majalisar dattawa kan kasuwanci da zuba jari.
Wani makusancinta, Patrick Ikorgor Okoroji, wanda ya ce ta mutu bayan dogon rashin lafiya da ba’a bayyana ba ya tabbatar da lamarin. Sanatar ta rasu tana da shekara 63 a duniya, jaridar The Sun ta ruwaito.
Wani hadimin marigayiyar wanda ya sake tabbatar da lamarin ya nuna bakin ciki da shiga kagauta.
KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Abba Kyari ya kamu da Coronavirus
A wani labari na daban, mun ji cewa majalisar wakilan tarayya ta tabbatar da cewa ta na bincike a game da wata wasika da ake tunanin ta fito daga ofishin Abba Kyari a fadar shugaban kasa.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa ‘yan majalisa su na bincike tare da duba ingancin takardar da ake zargin Abba Kyari ya aikowa shugabanta Rt. Hon. Femi Gbajabiamila.
Jama’a sun ga wannan takarda da ake kyautatata zaton fadar shugaban kasa ta aikowa Kakakin majalisar a game da matakan da ya kamata a dauke game da cutar COVID-19.
Ko da cewa wannan takarda ta sirri ce, mun ji labari mutane sun ci karo da ita a shafukan sada zumunta irinsu Facebook da kuma Tuwita a cikin farkon wannan makon.
A wannan wasika, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya zargi wasu ‘Yan majalisa da kin bari a duba su yayin da su ka iso filin jirgin saman Najeriya daga kasashen waje.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng